Tirelar Dangote Ta Markaɗa Ɗan Acaɓa har Lahira yayin da Suka yi Karo

Tirelar Dangote Ta Markaɗa Ɗan Acaɓa har Lahira yayin da Suka yi Karo

  • An samu wani mummunan hadarin babbar mota da ya jawo asarar rai da jikkata rayuka a wani yanki na jihar Legas
  • An ruwaito cewa babbar motar kamfanin Dangote ce ta yi karo da wani mai babur da ke sana'ar acaba yana dauke da wani mutum
  • Matukin motar da mataimakinsa sun cika rigarsu da iska bayan faruwar haɗarin kuma yan sanda sun yi karin haske kan halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - An samu wani mummunan haɗari tsakanin tirelar Dangote da wani mai acaba dauke da mutum a bayan babur.

An ruwaito cewa hadarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban wannar shekarar.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke Bobrisky da tsakar dare yana shirin guduwa daga Najeriya

Lagos
Motar Dangote ta markada dan acaba a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar the Nation ta wallafa cewa matukin motar ya gudu bayan faruwar hadarin kuma har yanzu ba a gano inda yake ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tirelar Dangote ta markaɗa ɗan acaɓa

A safiyar ranar Laraba wani dan acaba ya kwanta dama bayan karo da ya yi da motar Dangote.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da hanya ta cika da al'umma a wani yanki na jihar Legas.

Punch ta ruwaito cewa jami'an yan sanda sun dauki gawar dan acaɓan yayin da motar da markaɗa shi har lahira.

An kai wanda ya jikkata asibiti

Shaidun gani da idon sun ce hadarin babbar motar ya jawo samun rauni mai muni ga mutumin da yake bayan dan acaban.

A karkashin haka, yan sanda sun garzaya da shi asibiti domin duba lafiyarsa da ba shi kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

An kama motar Dangote bayan hadari

Biyo bayan hadarin, matukin motar Dangote da wanda suke aiki a cikin motar sun cika rigarsu da iska.

Saboda haka jami'an yan sanda suka tafi da motar zuwa caji ofis domin bincike da kuma cigaba da neman matukin motar.

Ambaliya ta rusa gada a Oyo

A wani rahoton, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta rusa wata gada da ta haɗa ƙauyuka sama da 50 a wani yanki na jihar Oyo.

An ruwaito cewa mutanen yankin sun fara neman taimako da agajin gaggawa daga gwamnati domin cigaba da zirga zirga a kauyukan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng