Haraji a Wuraren Ibada: Malaman Addini Sun Dura kan Gwamnati

Haraji a Wuraren Ibada: Malaman Addini Sun Dura kan Gwamnati

  • An soki gwamnatin jihar Abia bayan gwamna ya sanar da fara karɓar haraji kan abubuwan da suka shafi ibada
  • Shugaba CAN da sakataren kungiyar sun rubuta takarda ga gwamnan jihar suna nuna kin amincewa kan lamarin
  • Haka zalika CAN ta fito da wata hanya da za a iya samun maslaha da warware maganar karɓar harajin da ake shiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - Shugabannin addinin Kirista sun yi Allah wadai da wata dokar haraji da gwamnatin jihar ta kirkiro.

An ruwaito cewa gwamnatin Alex Otto ta saka dokar haraji a kan coci da suka kafa alluna a cikin jihar Abia.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Gwamnan Abia
CAN ta soki gwamnan Abia kan saka haraji ga coci. Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban CAN na jihar, Rabaran Ojo Ojo Uduma da sakatarensa, Dr Francis Okere ne suka yi raddi ga gwamnatin Abia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar haraji a kan wuraren ibada

Malaman addinin Kirista sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta saka musu dokar haraji a kan alluna da suka kafa a kan tituna.

Shugaban CAN na Abia, Rabaran Ojo Ojo Uduma ya koka kan sakawa coci haraji a kan alluna da suka kafa a fadin jihar.

CAN ta yi watsi da dokar harajin Abia

Kungiyar CAN ta ce abin Allah wadai ne yadda ake ganin Abia a matsayin jihar Kirista amma a ce an saka haraji ga coci.

Sahara Reporters ta wallafa cewa Rabaran Ojo Ojo Uduma ya ce idan ba ana son su dauki gwamnan a matsayin makiyin addinin Kirista ba ya kamata ya sauya dokar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari sun bude wuta, da dama sun mutu

CAN ta bukaci a tattauna kan haraji

Shugabannin CAN a Abia sun ce suna shirye da tattaunawa da gwamnatin jihar a kan maganar sanyawa coci haraji kan alluna.

Sun ce za su jira gwamnan jihar kan martanin da zai bayar kuma suna masa fatan gamawa lafiya.

Bill Gates ya bukaci Tinubu ya kara haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shahararren mai kudi a duniya, Bill Gates ya yi bayanai kan haraji yayin wata ziyara zuwa Najeriya.

Bill Gates ya bayyana cewa kudin haraji da ake karba a Najeriya ya yi kadan kuma hakan ba zai kawo cigaba a kasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng