2025: Abba Ya Sanar da Cigaba da Daukar Daliban Kano zuwa Ƙasashen Waje

2025: Abba Ya Sanar da Cigaba da Daukar Daliban Kano zuwa Ƙasashen Waje

  • Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta yi bayani kan ɗaukar ɗalibai domin zuwa ƙasashen ketare da niyyar samun ilimi mai zurfi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci dalibai da suke da niyyar karatu a ketare su zauna cikin shiri domin daukarsu a zangon 2024/2025
  • Gwamnatin Kano ta sanar da haka ne yayin tarbar wasu daliban jihar da aka tura karatu kasar Indiya a filin jirgi na Malam Aminu Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi albishir ga dalibai masu niyyar tafiya kasashen ketare domin samun ilimi mai zurfi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf domin ɗaukar ɗalibai a zangon karatun 2024/2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi barazanar sauke sarakuna saboda rashin tsaro

Abba Kabir
Za a sake tura dalibai karatu waje a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa abin da gwamnan ya fada a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kai ɗaliban Kano kasashen waje

Gwamnatin Kano ta sanar da shirin daukar dalibai zuwa karatu kasashen ketare domin samun digiri na biyu.

Abba Kabir Yusuf da kansa ya sanar da fara daukar dalibai zuwa kasashen ketare a zangon karatu na 2024/2025.

Za a dauki dalibai 1,001 zuwa ketare da wasu jami'o'in Najeriya domin zurfafa ilimi a fannoni daban daban.

"Wajibi ne a kanmu mu tabbatar da cewa yan Kano sun samu damar faɗaɗa ilimi."

-Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano

Yan Kano da suka kammala karatu a waje

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa wasu yan asalin jihar sun dawo daga kasar Uganda bayan kammala karatu a can.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso, Peter Obi, Abba da jiga jigan NNPP suka hadu yayin tarbar dalibai

Ta kuma sanar da cewa a watannin Nuwamba da Disamba masu zuwa wasu daga cikin daliban jihar za su dawo gida.

Abba zai dauki daliban Kano aiki

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin ɗaukar wasu daliban jihar da suka dawo daga karatu a Indiya aiki.

Abba Kabir Yusuf ya yi wa daliban su 29 alkawari ne yayin da jagororin NNPP suka tarbe su bayan kammala digiri na biyu a fannoni daban daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng