'Yan Bindiga Sun Hallaka Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Manoma a Neja
- Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun buɗe wuta kan matafiya a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja
- Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka aƙalla mutane uku bayan sun tare motocinsu a kan hanyar Bangi-Kotonkoro
- Shugaban ƙaramar hukumar Mariga ya ɗora alhakin yawan hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa a yankin da ke kan iyaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Ƴan bindiga sun kai farmaki kan wasu matafiya a jihar Neja, suka hallaka aƙalla mutum uku.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a hanyar Bangi-Kotonkoro a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Mazauna garin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa harin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi a lokacin da mutanen ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaya daga cikin mutanen yankin da ya so a sakaya sunansa ya ce ƴan bindiga sun tare hanyar Bangi da Kotonkoro sannan suka buɗewa motoci wuta.
Wani da ya tsira da ransa, Alhaji Shehu, ya ce an kashe direban motarsa da wata mata da kuma wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim.
Mazauna yankin sun ce an kuma yi garkuwa da manoma a lokacin da suke girbin shinkafa a gonarsu.
Me hukumomi suka ce kan harin?
Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ba, amma shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Musa Kasuwa- Garba ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce hare-haren ƴan bindiga sun zama ruwan dare a yankin saboda iyaka da jihohin Zamfara, Kebbi da Kaduna ta hanyar Birnin Gwari.
Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sandan Mopol da ke Garagi a kauyen Yartsamiyar Jino da ke a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun farmaki sansanin ƴan sandan da ke a karamar hukumar Kankara a ranar Talata, 22 ga watan Oktobar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng