An Shiga Jimami bayan Sojojin Najeriya Sun Rasu a Wani Hatsari
- Wasu sojojin saman Najeriya sun gamu da hatsarin mota a kan hanyarsu ta zuwa babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024
- Aƙalla sojoji biyar ne suka rasa rayukansu a hatsarin motan wanda ya auku a Hawan Kibo da ke kan hanyar Jos zuwa Akwanga
- Rundunar sojojin sama wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bayyana cewa za ta tallafawa iyalan sojojin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Aƙalla sojojin saman Najeriya biyar ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Hawan Kibo da ke kan hanyar Jos zuwa Akwanga a ranar Talata.
An tattaro cewa sojojin da suka rasu sakamakon hatsarin na daga cikin waɗanda za su halarci wani taron wasanni a birnin tarayya Abuja.
Sojojin saman Najeriya sun yi hatsari
Mai magana da yawun NAF, Olusola Akinboyewa, ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa motar sojojin da suka mutu ta yi taho mu gama ne da wata babbar mota da ke tahowa.
Air Commodore Olusola Akinboyewa ya ce rundunar NAF za ta tallafawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu.
Ya ƙara da cewa ya kamata ƴan Najeriya su mutunta sirrin sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.
"Wannan mummunan lamari ya faru ne a kusa da Hawan Kibo da ke kan hanyar Jos zuwa Akwanga."
"Jami’an mu na kan hanyarsu ta zuwa wani taron wasanni ne a Abuja, sai motar su ta yi karo da wata babbar mota da ke tahowa."
"Muna kira ga jama'a da su mutunta sirrin iyalan sojojin da suka rasu a wannan lokaci mai wuya sannan su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba. Allah jiƙansu da rahama.
- Air Commodore Olusola Akinboyewa
An rasa rayuka a hatsarin mota
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 19 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Hawan Kibo da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.
Kakakin hukumar FRSC reshen Plateau, Peter Yakubu ya bayyana cewa dukkan fasinjojin da ke cikin motar da ta yi haɗarin sun riga mu gidan gaskiya.
Asali: Legit.ng