"Mun Kunyata Afirika": Obasanjo Ya Nuna Damuwa kan Kuskuren da Najeriya Ta Yi

"Mun Kunyata Afirika": Obasanjo Ya Nuna Damuwa kan Kuskuren da Najeriya Ta Yi

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana abin kunyar da Najeriya ta yi a idon duniya
  • Obasanjo ya ce Najeriya ta kunyata jinsin baƙaƙen fata da nahiyar Afirika saboda rashin shugabanci nagari
  • Sai dai ya nuna fatan cewa abubuwa za su gyaru a ƙasar nan idan aka gyara kura-kuran da aka tafka a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Najeriya ta ba jinsin baƙaƙen fata da nahiyar Afirika kunya saboda rashin shugabanci nagari.

Obasanjo ya ce duk duniya na kallon Najeriya a matsayin jigon baƙaƙen fata saboda irin ƙarfin da take da shi, amma rashin shugabanci nagari da rashin haɗin ya sanya ƙasar ta rasa wannan damar.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Ana murna, gwamna ya sanar da lokacin fara biyan N70,000

Obasanjo ya koka kan rashin shugabanci a Najeriya
Obasanjo ya damu kan rashin shugabanci nagari a Najeriya Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: UGC

Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar Leauge of Northern Democrats ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya faɗi matsalar Najeriya

Tsohon shugaban ƙasan ya zargi tsarin gwamnatin shiyya wanda aka yi kafin samun ƴancin kai a 1960, a matsayin ginshiƙin rashin hadin kai da ya daɗe a ƙasar nan, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

Obasanjo ya ce, duk da halin taɓarɓarewar da abubuwa suka yi a ƙasar nan, yana da fatan cewa abubuwa za su gyaru idan za a gyara kura-kuran da aka yi a baya.

"Nahiyar Afirka, baƙar fata da duk duniya suna ganin darajarmu. Lokacin da muka samu ƴancin kai, abin da suke kiranmu shi ne babbar giwa, amma yau haka lamarin yake?"

Kara karanta wannan

COAS: DHQ ta bayyana gaskiya kan batun nada mukaddashin hafsan sojin kasa

"Mun kunyatar da kanmu, mun kunyata jinsin baƙar fata, Afirika da duniya gaba ɗaya. Dole ne mu manta da abubuwan da suka faru a baya, kuma mu yi aiki domin daukaka Najeriya."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya faɗi ciwon da ya kama shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan cutar da ta taɓa kama shi ba tare da ya sani ba.

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya taɓa samun matsalar rashin ji ta kaso 25% cikin 100% ba tare da sanin cewa yana ɗauke da ciwon ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng