Gwamnan Sokoto Ya Yi Wa Fursunoni Afuwa, Ya ba Su Shawara

Gwamnan Sokoto Ya Yi Wa Fursunoni Afuwa, Ya ba Su Shawara

  • Gwamnan Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya tausayawa wasu daga cikin fursunonin da ke gidan gyaran hali na jihar da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya yi afuwa ga fursunoni 113 waɗanda aka yankewa hukunci daban-daban a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024
  • Gwamnan ya kuma shawarci fursunonin da aka saki da su zama jakadu nagari na gidan gyaran halin yayin da suka koma rayuwa cikin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi afuwa ga fursunoni 113 da ke gidan gyaran hali na Sokoto.

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi afuwar ne a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024 domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi barazanar sauke sarakuna saboda rashin tsaro

Gwamnan Sokoto ya yi wa fursunoni afuwa
Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa fursunoni 113 afuwa a Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Twitter

Gwamnan Sokoto ya tausayawa fursunoni

Gwamnan ya samu wakilcin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Nasiru Binji, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ahmed ya ce afuwar ta yi daidai da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.

"A cikin fursunonin da aka yi wa afuwa, an saki guda 67 ba tare da wani sharaɗi ba, yayin da aka mayar da hukuncin kisa guda 22 zuwa ɗaurin rai-da-rai."
"Bugu da ƙari, fursunoni 22 da ke zaman ɗaurin rai da rai, an rage wa’adin zuwa shekara 25, sannan fursunoni biyu an rage musu hukuncin shekara biyu."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Wace shawara gwamnan ya ba su

Gwamnan ya umarci fursunonin da aka saki da su zama jakadu nagari na gidan gyaran halin yayin da suke komawa cikin al’umma, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

"Ka da ku tsaya baya": Gwamna ya fito ya ba matasan Najeriya muhimmiyar shawara

Ya kuma sanar da bayar da gudummawar tsabar kuɗi N50,000 ga kowane fursunonin 67 da aka sako don taimaka musu su fara sabuwar rayuwa.

Gwamnan Sokoto ya rage farashin kayan abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya karya farashin shinkafa da wasu kayan masarufi da gwamnatinsa ta sayo domin sauƙaƙawa al'umma.

Gwamna Aliyu ya rage kaso 55% na farashin buhun shinkafa da wasu kayan abincin da aka sayo domin ragewa al'umma raɗaɗin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng