Yadda Aka Cafke Bobrisky da Tsakar Dare Yana Shirin Guduwa daga Najeriya

Yadda Aka Cafke Bobrisky da Tsakar Dare Yana Shirin Guduwa daga Najeriya

  • An kara samun bayanai kan yadda aka cafke shahararren ɗan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky yana shirin guduwa
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an cafke Idris Okuneye ne da tsakar dare yana ƙoƙarin tsallake iyakokin Najeriya da Benin
  • Hukumar shige da ficen Najeriya (NIS) ce ta cafke Bobrisky kuma ta bayyana matakin da za ta dauka a kansa bayan an maido shi gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - A ranar Litinin aka samu bayanai kan cewa an cafke shahararren dan daudu da aka fi sani da Bobrisky.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana yadda aka kama dan daudun da misalin karfe 1:30 na dare yana ƙoƙarin guduwa.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Bobrisky
Yadda aka kama Bobrisky a Seme. Hoto: @bobrisky222
Asali: Instagram

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lauyan Bobrisky ya isa wajen da aka kama shi domin tambayar dalilin cafke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama Bobrisky cikin dare

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Litinin da misalin karfe 1:30 na dare Bobrisky ya isa iyakokin Najeriya da Benin da ke Seme.

Vanguard ta ruwaito cewa dan daudun ya isa wajen ne a cikin wata kirar Marsandi sai jami'an lafiya a iyakokin suka dakatar da shi.

Bayan haka kuma sai ya mika fasfo din shi domin a tantance shi. Ga abin da shaidar gani da ido yake cewa:

"Yana mika fasfo din shi sai aka gano Bobrisky ne daga nan kuma aka kira babban jami'in shige da fice.
Daga nan aka lallaɓi Bobrisky ya je ofishin babban jami'in inda aka rika masa tambayoyi har karfe 4:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Yaushe za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya? TCN ya yi bayani

Bayan kammala bincike a wajen sai kuma aka tafi da Bobrisky zuwa Legas domin a cigaba da masa tambayoyi"

- Shaidar gani da ido

Dalilin kama Bobrisky a iyakar Seme

A lokacin da aka kama Bobrisky, lauyansa ya je wajen domin bincike kan dalilin da ya sa hukumar shige da fice ta cafke shi.

Jami'in yada labaran hukumar shige da fice, Kenneth Udo ya bayyana cewa an kama Bobrisky ne saboda bincike da ake kan zamansa a gidan yari.

An bude iyakokin Najeriya da Nijar

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya da kasar jamhuriyyar Nijar.

An ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni bude iyakokin sama da kuma na tudu da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng