NDLEA: Majalisa Ta Dauki Mataki kan Zargin Kama Kwayoyi a Gidan Sanata

NDLEA: Majalisa Ta Dauki Mataki kan Zargin Kama Kwayoyi a Gidan Sanata

  • Majalisar dattawa ta damu kan zargin da hukumar NDLEA ta yi wa Sanata Oyelola Yisa Ashiru na samun ƙwayoyi a gidansa
  • Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi wanda zai binciki zargin da ake yi wa sanatan mai wakiltar jihar Kwara ta Kudu
  • Kwamitin wucin gadin da aka kafa domin gudanar da binciken zai kammala aikinsa ne nan da mako ɗaƴa mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta ɗauki mataki kan zargin da hukumar NDLEA ta yi wa Sanata Oyelola Yisa Ashiru na samun ƙwayoyi a gidansa.

Majalisar dattawan ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki zargin da hukumar ke yi wa sanatan wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye.

Kara karanta wannan

"Sun zama maboyar miyagu:" FCTA ta bayar da wa'adin kammala gine gine a Abuja

Majalisa ta kafa kwamiti kan zargin NDLEA
Majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki zargin NDLEA kan sanata Ashiru Hoto: Nigerian Senate, NDLEA
Asali: Facebook

Majalisar dattawan ta dauki matakin ne a ranar Talata bayan da Sanata Ashiru ya gabatar da wani ƙudiri, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NDLEA ta zargi Sanata da harkar ƙwayoyi

Tun da farko dai hukumar NDLEA ta ce ta gano kwayoyi a gidan Sanata Ashiru kuma ta kama wasu hadimansa guda biyu a shekarar 2023, zargin da ya musanta.

Zargin na NDLEA ya zo ne bayan sanatan mai wakiltar Kwara ta Kudu ya ce hukumar ita ce "hukumar gwamnati mafi cin hanci da rashawa" a ƙasar nan.

Yayin da yake magana a zauren majalisar dattawa, Sanata Ashiru ya ce NDLEA na ƙoƙarin hana shi magana a matsayinsa na sanata kan al'amura ta hanyar jifarsa da zargin da bai da tushe.

"Ina so in tabbatar da cewa ban san menene tabar wiwi ba, ba na shan barasa. Domin kariyata da ta sauran Sanatoci, dole ne mu yi wani abu game da wannan."

Kara karanta wannan

NDLEA: Sanata ya yi kakkausan martani kan zargin kama kwayoyi a gidansa

- Sanata Oyelola Yisa Ashiru

Majalisa ta kafa kwamitin binciken Sanata

Da yake mayar da martani, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce akwai buƙatar wani kwamitin wucin gadi da zai binciki lamarin cikin tsanaki, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Daga ƙarshe an naɗa Enyinnaya Abaribe, Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu a matsayin shugaban kwamitin wucin gadi.

Ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa cikin mako guda.

Shugaban majalisa ya kare Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Apkabio ya tabbatarwa yan kasar nan cewa ba a gwamnatin Bola Tinubu aka samu matsalar tattalin arziki ba.

Apkabio ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba, ya jaddada cewa matsalar tattalin arzikin kasar nan ya samo asali ne daga gwamnatocin baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng