Sankara: Labari Ya Sauya, Hisbah Ta Magantu kan Zargin Kwamishinan Jigawa

Sankara: Labari Ya Sauya, Hisbah Ta Magantu kan Zargin Kwamishinan Jigawa

  • Yayin da ake zargin kwamishina da lalata da matar aure, wani jami'in hukumar Hisbah ya yi magana
  • Malam Aliyu Dakata ya wanke kwamishinan ayyuka na musamman, Auwal Danladi Sankara daga zargin da ake yi masa
  • Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi wa kwamishinan da lalata da matar aure a wani gidansa da ba a kammala ba a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar Hisbah a Kano ta yi amai ta lashe kan zargin kwamishina a jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara.

Jami'in hukumar ya janye zargin da ake yi kan kwamishinan ayyuka na musamman, Sankara da lalata da matar aure.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata da kwamishinansa kan karairayi da ya kafta masa, ya ba da umarni

Hisbah ta yi magana kan zargin kwamishina da zargin lalata
Hukumar Hisbah ta lashe amanta kan zargin kwamishina da lalata matar aure a Kano. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Facebook

Hisbah ta magantu kan zargin kwamishina, Sankara

Channels TV ta ce jami'in mai suna Malam Aliyu Dakata ya ce babu wani zargi kan Sankara kamar yadda ake yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan yada rahotannin da ke cewa an kama kwamishinan da wata matar aure da zargin lalata.

Wani jami'in hukumar ne ya tabbatar da haka inda ya ce mijin matar ne ya shigar da korafi kan haka inda yake zarginsu.

Daga bisani, kwamishinan ya yi martani kan zargin inda ya ce ana ƙoƙarin bata masa suna ne kawai.

Sankara ya yi Allah wadai da lamarin inda ya ce zai dauki matakin shari'a kan masu neman ci masa mutunci.

Sai dai a cikin wani hira, jami'in Hisbah, Dakata ya wanke kwamishinan inda ya ce babu zargin komai a kansa.

"Lokacin da muka iso wurin, mun samu Tasleem a cikin motarta tana amsa kira shi kuma Sankara yana tsaye a cikin gidan da ba a kammala ba, babu wani abu da suke yi na lalata."

Kara karanta wannan

Hisbah ta ayyana neman kwamishina ruwa a jallo kan zargin lalata a Kano

- Malam Aliyu Dakata

Lauyan matar ya fadi yadda abin yake

Lauyan matar, Tasleem, Barista Rabiu Shuaibu ya ce mijinta ya rabu da ita watanni 10 da suka wuce inda take kasuwanci domin daukar nauyin 'ya'yanta.

Ya ce Tasleem tana siyar da abinci inda ta kawowa Sankara da ya bukata bata sani ba mijinta yana bibiyarta.

Hisbah na neman kwamishina ruwa a jallo

A baya, kun ji cewa Hukumar Hisbah ta fara neman dakataccen kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwal Sankara ruwa a jallo.

Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun yi koƙarin zaman sulhu amma Auwal Sankara bai halarta ba.

Ya buƙaci dakataccen kwamishinan ya miƙa ƙansa ga jami'an hukumar Hisbah domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.