Hukumar SON Ta Hango Illar Amfani da Gas din CNG, An Turawa Magidanta Gargadi

Hukumar SON Ta Hango Illar Amfani da Gas din CNG, An Turawa Magidanta Gargadi

  • Hukumar kula da ingancin kayyaki ta kasa (SON) ta gargadi jama’a wajen taka tsan-tsan wajen amfani gas din CNG
  • Shugaban SON, Dr Ifeanyi Okeke ya ce amfani da gas din cikin kowace irin tukuna zai iya haddasa mummunar gobara
  • Gargadin na zuwa bayan an samu fashewar wata motar CNG da ake zargin an dura a tukunyar gas mara inganci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Hukumar kula da ingancin kayyaki ta kasa (SON) ta gargadi jama’ar kasar nan kan amfani da gas din CNG saboda an gano tarin matsalolin da ya ke dauke da shi.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ambaliya ta karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Haka kuma hukumar ta kara jan kunnen jam’a kan amfani da gas din LPG wajen girki domin kare rayukan jama’a daga matsaloli da dama.

GAS CNG
SON ta gargadi jama'a kan amfani da gas din CNG Hoto: Bat Arojuraye
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa hukumar SON ta jaddada wa jama’an kasar nan cewa ba kowane tukunyar gas din girki ne za a dura gas din CNG ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar SON ta fadi illar amfani da CNG

Jaridar The Nation ta tattaro cewa hadarin da ya afku da gas din CNG a Benin ya bayyana illar amfani amfani da gas din da tukunya mara inganci.

Binciken da SON ta yi ya gano cewa an amfani da tukunyar gas din da aka hada a gefen titi ba tare da amfani da kwarewa ba ne ya haddasa matsalar.

CNG: SON ta shawarci yan kasa

Darakta Janar kuma shugaban hukumar SON na kasa, Dr Ifeanyi Okeke ya nemi jama’a su kare rayukansu da na jama’a wajen amfani da gas din CNG.

Kara karanta wannan

"Sun zama maboyar miyagu:" FCTA ta bayar da wa'adin kammala gine gine a Abuja

Dr Ifeanyi Okeke ya bayyana cewa iskar gas din CNG ya fi fetur hadari matuka idan aka kwatanta da fetur.

Direbobi sun guji amfani da CNG

A wani labarin kun ji cewa duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na ganin an rungumi amfani da gas din CNG, direbobi sun gujewa mayar da motocinsu mai amfani da gas.

Man iskar gas na CNG yana da arha wanda hakan ya sanya zama makwafin man fetur domin yin amfani da shi a motoci wanda ya sa gwamnati bullo da shirin PCNGi don a koma amfani da sabon gas din.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.