Ana Rade Radin Rigimar Abba da Kwankwaso, an Kori Yan Jaridu daga Gidan Gwamnati
- Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta dakatar da yan jaridu 14 daga aiki a gidan gwamnatin jihar
- Rahotanni sun tabbatar da wadanda abin ya shafa suna wakiltar gidajen jaridu ko rediyo daban-daban a cikin gidan gwamnatin
- Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir a Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da yan jaridu 14 daga daukar rahoto a gidan gwamnati.
Gwamantin jihar da umarci dukan wadanda abin ya shafa da su koma wuraren aikinsu domin a sauya su da wasu.
Abba ya sallami wasu yan jaridun gidan gwamnati
Kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Daily Trust ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Dawakin Tofa bai fayyace dalilin dakatar da yan jaridun ba inda ya umarce su da su bi umarnin da aka ba su.
Dawakin Tofa ya godewa yan jaridun kan irin gudunmawar da suka bayar a cikin shekara daya da wasu watanni da gwamnatin Abba Kabir ta yi.
Jawabin gwamnatin Abba Kabir Yusuf
"Ina amfani da wannan dama wurin yi muku godiya kan gudunmawar da kuka bayar a wannan gwamnati tsawon shekara daya da watanni."
"Abin takaici, lokacin da na ke kasar Serbia wasu abubuwa sun faru da ke buƙatar daukar wasu matakai."
"Wannan ba shi ne karshen mu'amala a tsakaninmu ba, zamu cigaba da tafiya a hukumance ko akasin haka."
- Cewar sanarwar
Yan jaridun da abin ya shafa a Kano
Daga cikinsu akwai daraktan wayar da kan al'umma, Aliyu Yusuf da jami'in hulda da jama'a, Sani Suraj Abubakar da Adamu Dabo da ke kai rahoto ga gidan rediyon Pyramid (FRCN).
Sai kuma Naziru Yau daga ARTV da Sadiq Sani AA daga ARTV da Rabiu Sunusi da Umar Sheka daga rediyon Freedom duk a cewar Premium Times.
Har ila yau, akwai Jabir Dan’abba daga gidan rediyon Nasara sai Labara Sound da Simon daga AIT sai Nasiru Danhaki daga NTA da direbansu, Abdullahi Sule.
Akwai Murtala Baba Kusa daga gidan rediyon Express da Ibrahim Muazzam daga rediyon Kano.
Abba ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 60
Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sakon murnar ranar haihuwa ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Hakan na zuwa ne duk da yawaitar kiran cewa ya kamata Abba Kabir Yusuf ya bijirewa madugun Kwankwasiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng