Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci kan Bukatar Rusa EFCC da Gwamnoni 16 Suka Shigar

Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci kan Bukatar Rusa EFCC da Gwamnoni 16 Suka Shigar

  • Hukumar EFCC da wasu gwamnoni 16 na zaman jiran hukuncin da Kotun Koli za ta yanke kan rusa hukumar da ke yaki da rashawar
  • A cikin wata kara da suka gabatar, gwamnonin sun ce an saba kundin tsarin mulkin Najeriya wajen kafa hukumar EFCC a 2004
  • Kwamitimin alkalan kotun mai mutane biyar, ya sanya ranar 22 ga Oktoba domin yanke hukuncin hallaci ko haramcin kafuwar EFCC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yau Talata, 22 ga watan Oktoba ne ake sa ran Kotun Koli za ta yi hukunci kan karar da wasu gwamnoni 16 suka shigar na kalubalantar dokar da ta kafa hukumar EFCC.

Gwamnonin da kuma ita kanta EFCC na dakon hukuncin da Kotun Kolin za ta yanke, wanda zai tabbatar da halacci ko haramcin kafuwar hukumar yaki da rashawar.

Kara karanta wannan

Gyaran tattalin arziki: Manyan nasarori 5 da gwamnatin Tinubu ta samu a 2024

Kotun koli za ta yi hukuncin kan bukatar rusa EFCC da wasu gwamnoni 16 suka shigar
Kotun Koli za ta yi hukunci kan bukatar da wasu gwamnono suka shigar na rusa EFCC. Hoto: @SupremeCourtNg
Asali: Twitter

Gwamnoni na adawa da kafuwar EFCC

Gwamnonin sun nuna cewa wani hukunci da Kotun Koli ta yanke a shari'ar Dakta Joseph Nwobike da gwamnatin tarayya, ya fayyace asalin aikin EFCC, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin karar da suka shigar, gwamnonin sun ce yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa ce aka mayar da ita zuwa dokar da ta kafa EFCC.

A cewar gwamnonin, kafa hukumar EFCC bisa wannan doka ya sabawa sashe na 12 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ita Kotun Kolin ta tabbatar a baya.

Hukumar EFCC ta caccaki gwamnoni 16

A ranar Talata ne kwamitin alkalai mai mutane bakwai karkashin jagorancin Mai shari’a Uwani Abba-Aji, ya sanya ranar 22 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron karar.

Sai dai hukumar ta EFCC, ta nuna rashin jin dadin ta game da kiran da aka yi na yi wa hukumarsu garambawul, inda ta bayyana cewa masu karar na “jin zafin aikinta".

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, Tinubu ya shirya kakabawa 'yan Najeriya wani sabon haraji

Daraktan hulda da jama’a na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da Channels TV a safiyar ranar Litinin.

Uwujaren ya kare mahimmancin wanzuwar hukumar, inda ya bayyana cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya su yaki cin hanci da rashawa.

EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya nuna adawa kan kan yunkurin da wasu gwamnoni ke yi na ganin an soke hukumar EFCC.

Gwamna Fintiri, wanda ya bayyana cewa bai kamata a rusa hukumar EFCC ba, ya ce kamata ya yi ma a kara karfafa ta domin ta gudanar da aikinta yadda ya dace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.