Yaushe Za a Dawo da Wutar Lantarki a Arewacin Najeriya? TCN Ya yi Bayani
- Kamfanin rarraba wutar lantarki TCN ya yi bayani ga yan kasa kan halin da ake ciki bayan katsewar wutar lantarki a Arewa
- TCN ya bayyana cewa tun a ranar Lahadi da wuta ta dauke injiniyoyi suke ta kokarin samar da mafita kan lamarin har zuwa yanzu
- Legit ta tattauna da wani mai sayar da shinkafa domin jin yadda rashin wuta a Arewa ta shafi sana'arsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya yi bayani kan halin da ake ciki bayan daukewar wutar lantarki a yankin Arewa.
Tun ranar Litinin da asuba wuta ta katse a yankuna da dama inda al'umma suka koma cikin duhu.
Legit ta tatttaro bayanai da kamfanin TCN ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a Facebook a safiyar ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da ake ciki bayan dauke lantarki
Kamfanin TCN ya bayyana cewa tun da aka samu katsewar lantarki suka tura injiniyoyi domin shawo kan matsalar.
Sai dai cikin rashin sa'a, tun da suka fara ƙoƙarin shawo kan matsalar ba su gano bakin zaren ba kuma sun cigaba da ƙoƙarin a safiyar ranar Talata.
Kamfanin TCN ya ba yan Najeriya hakuri
Kamfanin TCN ya bayar da hakuri kan katsewar wutar lantarki ga gwamnatin Najeriya da dukkan yan kasa.
TCN ya tabbatar da cewa zai dawo da wutar lantarki a jihohin Arewa da zarar ya gano matsalar da kammala gyara.
Jihohin Arewa da ba su da lantarki
Rahotanni sun nuna cewa katsewar lantarki ta shafi dukkan jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Haka zalika kamfanin TCN ya bayyana cewa lamarin ya shafi yankuna da dama a Arewa maso Yamma.
Abin bai tsaya a nan ba, ya wuce har yankin Arewa ta Tsakiya inda al'umma suka shafe sama da sa'o'i 24 babu lantarki.
Legit ta tattauna da Shua'ibu Muhammad
Wani mai sayar da shinkafa, Shua'ibu Muhammad ya zantawa Legit cewa rashin wuta ya sanya fara tashin farashin shinkafa.
A cewarsa, farashin shinkafa ya fara sauka a kwanan nan amma rashin wuta ya fara mayar da lamarin baya a jihar Gombe.
TCN na raba wuta ga kasashen Afirka
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin TCN ya bayyana cewa akwai wasu ƙasashen Afirka da yake ba wutar lantarki kuma suna shafe sa'o'i 24 ba tare da katsewa ba.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin yan Najeriya inda suke ganin bai kamata a ce wasu ƙasashe na samun wuta sama da yadda suke samu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng