Gwamna Ya Fusata da Kwamishinansa kan Karairayi da Ya Kafta Masa, Ya ba da Umarni

Gwamna Ya Fusata da Kwamishinansa kan Karairayi da Ya Kafta Masa, Ya ba da Umarni

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya fusata da wani kwamishina a jihar kan ayyukan makaranta
  • Gwamna Fubara ya nuna damuwa kan karairayi da kwamishinan ilimi ya yi masa game da gyaran makaranta
  • Fubara ya caccaki kwamishinan kan yaudararsa da ya yi da cewa aikin ya yi nisa da 70% wanda ya fahimci karya ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya caccaki wani kwamishinansa kan aikin makaranta.

Gwamnan ya fusata kan karairayi da kwamishinan ya rika masa game da ayyukan gyaran makaranta.

Gwamna ya fusata da kwamishinansa kan yi masa karya
Gwamna Siminalayi Fubara ya soki kwamishina a Rivers kan tafka masa karya. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Rivers: Gwamna ya fusata da karyar kwamishinansa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatarensa, Nelson Chukwudi ya fitar a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sankara: Labari ya sauya, Hisbah ta magantu kan zargin kwamishinan Jigawa da lalata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce gwamnan ya fusata da kwamishinan ilimi kan wani aiki a makaranta da ke karamar hukumar Okrika.

Gwamna Fubara ya nuna damuwa bayan kai ziyarar gani da ido a makarantar a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024.

Fubara ya fusata ne bayan karya da kwamishinan ya yi masa cewa aikin ya yi nisa da kaso 70.

"Na samu rahotanni daga kwamishinan kan aikin, na yi tunanin zuwa da kai na saboda wannan mazaba ta ce."
"Maganar gaskiya, ina son Okrika saboda ya kamata na zo da kaina na ga tafiyar aikin da kuma ingancinsa."
"Gaskiya, ban gamsu ba ko kadan, kwamishinan ya ce an yi nisa da 70% kuma abin ba haka ya ke ba."

- Siminalayi Fubara

Gwamna Fubara zai dauki mataki

Fubara cikin fushi ya ce zai kira wata ganawa da yan kwangilar domin ba su umarni kan aikin da yake tafiyar hawainiya.

Kara karanta wannan

Kaico: Zargin aikata aikin assha da matar aure ya sa an dakatar da kwamishina a Jigawa

Ya bukaci bin dokar aikin da aka bayar da kuma tabbatar da kammala shi a lokacin da ya dace kamar yadda aka yi yarjejeniya.

Fubara zai biya ma'aikata N85,000 a wata

Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kere N70,000, ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Ribas.

Shugaban ma'aikatan jihar, George Nwaeke ya ce gwamnan ya amince da sabon albashin ne yayin ganawa da ƴan kwadago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.