Ministoci Sun Firgita da Dawowar Tinubu, An Fadi Lokacin da Ake Ganin Zai Kori Wasu
- Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar Bola Tinubu ya sallami wasu daga cikin Ministoci a wannan mako
- Tun bayan dawowarsa a karshen mako, ake hasashen komai zai iya faruwa da wasu Ministoci da masu mukamai
- Hakan bai rasa nasaba da doguwar ganawa da Tinubu ya yi da hadimarsa a bangaren kula da kokarin masu muƙamai, Hadiza Bala Usman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kwanaki kadan da dawowar Bola Tinubu an sake maganar sallamar wasu Ministoci.
Rahotanni sun ce akwai yiwuwar shugaban ƙasar ya kaddamar da korar Ministocin a wannan mako da muke ciki.
Tinubu ya yi ganawa da Hadiza Bala Usman
The Guardian ta ce Tinubu ya gana da hadima a bangaren kula da ayyukan masu mukamai, Hadiza Bala Usman a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan bai rasa nasaba da yawan korafi kan mafi yawan Ministoci a wannan gwamnati ta jam'iyyar APC.
Al'umma da dama na nuna damuwa kan rashin katabus na wasu Ministoci ke yi a kasar wanda suka cancanci a sauya su.
Ofishin kula da ayyukan Ministocin da tsare-tsare yana tabbatar da wanda duba zuwa ga kokarin wadanda aka nadan.
Har ila yau, zai kuma ba da bahasi kan Ministan da ya kamata a kora ko kuma a rike a gwamnatin, Vanguard ta ruwaito.
Ana hasashen Bola Tinubu zai kori Ministoci
Bayan dawowar Tinubu a karshen mako, an tabbatar cewa wasu Ministoci sun firgita matuka a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024.
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun tabbatar cewa Hadiza Bala Usman ta gabatar da kokarin Ministocin ga Tinubu.
Ministocin sun tsorata ne a jiya Litinin bayan doguwar ganawa da Tinubu ya yi da Hadiza Bala Usman.
Tinubu ya shiga ofis bayan gama hutu
A wani labarin, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa kan halin da ake ciki bayan dawowar shugaba Bola Ahmed Tinubu daga hutu daga ketare .
Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ya iso Najeriya bayan ya shafe mako biyu cikin hutu na musamman Birtaniya da Faransa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng