Wani Ɗan Bindiga Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Suke Amfani da Kudin Fansa
- Dakarun ƴan sanda sun kama wasu ƴan bindiga bakwai da suka addabi Abuja da jihohin Kaduna da Neja
- Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya ce kudin fansar da suke karɓa na karewa ne wurin neman mata da shaye-shaye
- Kwamishinan ƴan sandan Abuja, CP Tunji Diru ya ce ƴan sanda sun hallaka jagoran ƴan bindigar mai suna Mallam a musayar wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗaya daga cikin ƴan bindigar da dakarun ƴan sanda suka kama, Abdulrahman Adamu ya yi bayanin yadda suke kashe kuɗin fansa.
Abdulrahman ya ce yana karar da kason kudin da ya samu bayan sun karɓi fansa ne wajen shaye-shaye da kuma neman mata.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ɗan bindigar na ɗaya daga cikin mutum bakwai da kwamishinan ƴan sandan Abuja, Tunji Disu ya tabbatar da kama su ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun cafke mutum 7
Disu ya bayyana sunayen wadanda aka cafke da Abdulrahman Giwa, Baba Hassan, Mohammed Dahiru, Abubakar Bature Dayi, Abubakar Kadiri da ake kira Dare, da Kabiru Ibrahim.
Sauran waɗanda yan sanda suka cafke sun hada da Ya’u Adamu da Hussani Ori wanda aka fi sani da Mugu.
Kwamishinan ƴan sanda ya ce ƴan bindigar sun jima suna addabar mutane a yankunan Abuja, da jihohin Kaduna da Neja.
CP Disu ya kuma bayyana cewa ƴan sanda sun kashe shugaban tawagar mai suna Mallam, tare da wasu takwas a musayar wuta.
Ɗan bindiga sun faɗi yadda suke kashe kudi
Da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga hannu, Abdulrahman Adamu ya amsa cewa ya samu makudan kudade a harkar garkuwa da mutane.
Ya ce daga cikin kudin da ya samu har da N600,000 a aiƙin karshe da suka yi kafin a kama shi, cewar rahoton Leadership.
Da aka tambaye shi ta wace hanya yake amfani da kuɗaɗen da ya samu, wanda ake zargin ya ce, "Neman mata da shaye-shaye."
Yan bindiga sun tare titin Funtua-Gusau
A wani rahoton kuma ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoban 2024.
A yayin harin, ƴan bindigan sun hallaka mutum biyu sannan suka yi garkuwa da matafiya masu yawa zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng