Hisbah Ta Ayyana Neman Kwamishina Ruwa a Jallo kan Zargin Lalata a Kano

Hisbah Ta Ayyana Neman Kwamishina Ruwa a Jallo kan Zargin Lalata a Kano

  • Hukumar Hisbah ta fara neman dakataccen kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwal Sankara ruwa a jallo
  • Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun yi koƙarin zaman sulhu amma Auwal Sankara bai halarta ba
  • Ya buƙaci dakataccen kwamishinan ya miƙa ƙansa ga jami'an Hisbah domin gurfanar da shi a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Hukumar Hisbah ta Kano ta ayyana neman dakataccen kwamishinan ayyuka na musamman na Jigawa, Auwal Danladi Sankara ruwa a jallo.

Hisbah ta fara neman kwamishinan ruwa a jallo ne bayan ya ƙi amsa gayyatar zaman sulhu da aka masa kan zargin lalata da matar aure.

Sheikh Daurawa da Auwal Sankara.
Hisbah ta fara neman Auwal Danladi Sankara ruwa a jallo Hoto: Sheikh Aminu Daurawa, Auwal D. Sankara
Asali: Facebook

Auwal Sankara dai ya musanta zargin da ake masa kuma ya yi barazanar maka hukumar Hisbah a gaban kotu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar Hisbah ta yi kokarin yin sulhu

Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun jira zuwan dakataccen kwamishina tsawon awanni amma ba shi ba wakilinsa.

Ya ce hakan ya sa Hisbah ba ta da wani zaɓi face ta ba da umarnin kamo shi a duk inda aka ganshi.

Sheikh Daurawa ya ce sun ba da belin Auwal Sankara bayan kama shi, amma kuma ya ki mutunta alƙawarin halartar zaman da aka shirya domim yin sulhu.

Hisbah ya nemi Auwal Sankara ya mika kansa

Da yake zantawa da manema labarai, Daurawa ya ce:

"Aikin Hisbah shi ne yin sulhu, idan hakan ba ta yiwu ba sai mu miƙawa kotu, a wannan kes din, shi Nasiru Bulama yana zargin Auwal Sankara da lalata da matarsa.
"Hakan ya sa muka nemi su dawo yau a zauna a yi sulhu, ɓangaren Nasiru ya zo da lauyoyinsa amma ita matar ba ta zo ba, babarta ba ta zo ba, shi ma (Auwal Sankara) bai zo ba."

Kara karanta wannan

Sankara: Labari ya sauya, Hisbah ta magantu kan zargin kwamishinan Jigawa da lalata

Sheikh Daurawa ya yi kira ga dakataccen kwamishinan ya kawo kansa ofishin Hisbah tun wuri domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Abubuwa 5 game da Auwal Sankara

A wani labarin kuma jami'an Hisbah sun cafke Auwal Ɗanladi Sankara, kwamsihinan ayyuka na mumman a Jigawa kan zargin lalata da matar aure.

Bayan haka ne Legit Hausa ta zaƙulo muku wasu mihimman bayanai game da kwamishinan wanda ya faɗa komar Hisbah a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262