Bobrisky: Asirin Shahararren Ɗan Daudu Ya Tonu Yana Shirin Tserewa a Iyakar Najeriya

Bobrisky: Asirin Shahararren Ɗan Daudu Ya Tonu Yana Shirin Tserewa a Iyakar Najeriya

  • Rahotonni na nuni da cewa jami'an shige da ficen Najeriya sun cafke shahararren dan daudu da aka fi sani da Bobrisky
  • An cafke dan daudun ne yana kokarin ficewa daga Najeriya ana tsaka da bincikensa kan wasu laifuffuka da ake zarginsa da yi
  • Wata majiya mai tushe ta tabbatarwa Legit cewa an cafke Bobrisky ne a tsakanin iyakokin tarayyar Najeriya da kasar Benin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa an cafke shahararren dan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.

An ruwaito cewa Idris Okuneye ya shiga hannun jami'an shige da ficen Najeriya ne yayin da yake kokarin ketare iyakar kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, Tinubu ya shirya kakabawa 'yan Najeriya wani sabon haraji

Bobrisky
An kama dan daudu yana kokarin fita daga Najeriya. Hoto: Bobrisky
Asali: Instagram

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an zargi dan daudun ne yana neman guduwa domin kaucewa bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken da ake yi wa Bobrisky

Tun bayan fitar Bobrisky daga kurkuku aka fara ce-ce-ku-ce a kan ko ya yi zaman gidan yari kamar sauran fursunonin da aka daure.

Hakan kuma ya zo ne saboda wasu bayanai da aka samu na zargin cewa shahararren dan daudun ya bayar da cin hanci ga jami'an gidan yari.

A dalilin haka, majalisar wakilai ta kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru da Bobrisky a gidan yari.

An cafke shahararren dan daudu

Leadership ta ruwaito cewa ana tsaka da bincike a kan Bobrisky ne ya yi yunkurin tserewa daga Najeriya.

Sai dai kafin ficewarsa a iyakarsa Najeriya da Benin aka kama shi a yankin Seme a safiyar Litinin kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

A yanzu haka dai kallo ya koma kan jami'an shige da ficen Najeriya domin ganin bayani ko hukuncin da za su yi a kan lamarin.

Yan bindiga sun kai hari Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai mummunan hari a karamar hukumar Akwa ta Kudu a jihar Anambra a Kudancin Najeriya.

An ruwaito cewa yan bindigar sun kai harin ne a wata mota kirar Jeep kuma sun bude kan mai uwa da wabi, suka kashe rayuka goma nan take.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng