Sarkin Rano Ya Mika Bukatarsa wajen Gwamna Abba bayan An Nada Shi Sarauta

Sarkin Rano Ya Mika Bukatarsa wajen Gwamna Abba bayan An Nada Shi Sarauta

  • Sarkin Rano, Muhammadu Isa Umaru ya miƙa buƙatar mutanen yankinsa a gaban gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Sarkin ya buƙaci gwamnann ya soke kwangilar aikin wani titi da ya ba da saboda wanda aka bai aikin yana tafiyar hawainiya
  • Ya kuma buƙaci gwamnan da ya kawo musu ɗauki kan matsalar ƙarancin ruwa da suka daɗe suna fama da ita a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Rano, Muhammadu Isa Umaru, ya miƙa kokensa a gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Sarkin na Rano ya buƙaci Gwamna Abba da ya soke aikin titin kilomita biyar da ya bayar a yankin tare da mayar da shi ga wani ɗan kwangila domin a gaggauta aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Tsohon SSG ya fadi abin da ya dace 'yan Najeriya su yi wa Tinubu kan tsadar rayuwa

Sarkin Rano ya mika bukata wajen Gwamna Abba
Sarkin Rano ya bukaci Gwamna Abba ya kawo musu dauki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Muhammad Isa Umaru ya yi wannan roƙon ne a lokacin tabbatar da naɗinsa tare da miƙa masa sandar mulki, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Rano ya miƙa buƙata ga Gwamna Abba

Sarkin ya ce ɗan kwangilar da ke kula da aikin ba zai iya ba, domin haka akwai bukatar a mayar da shi hannun wani ɗan kwangila daban.

Sarkin mai daraja ta biyu ya kuma yi kira ga gwamnan kan buƙatar samar da mafita mai ɗorewa kan matsalar ƙarancin ruwa da aka daɗe ana fama da ita a yankin.

"Hanyar mai tsawon kilomita biyar tana da matuƙar muhimmanci ga mutanen Rano amma abin takaici ɗan kwangilar da ke kula da aikin ba zai iya gudanar da ita ba."
"Har ila yau, muna fuskantar matsalar ƙarancin ruwa kuma gwamnatocin da suka shuɗe sun yi ƙoƙarin magance matsalar ta hanyar jawo ruwa daga Tiga."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya feɗe gaskiya kan rigimar shugabancin PDP na ƙasa

"Amma akwai wani tsauni da ke kusa wanda zai iya samarwa da wadata Rano da kewaye da ruwan da ake buƙata."

- Muhammadu Isa Umaru

Gwamna Abba ya tura saƙo ga Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tura sakon murnar ranar haihuwa ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce a tsawon shekaru, madugun na kwankwasiyya ya nuna shi jarumi ne, mai gaskiya da taimakon al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng