Kotu Ta Sa Ranar Sauraron Shari'ar Hisbah da Kwamishina kan Zargin Lalata da Matar Aure

Kotu Ta Sa Ranar Sauraron Shari'ar Hisbah da Kwamishina kan Zargin Lalata da Matar Aure

  • Babbar kotun shari'ar Muslunci da ke zamanta a Kano ta sanya ranar fara sauraren shari'ar da Hisbah ta shigar gabanta
  • Hukumar ta gurfanar da dakataccen kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara gaban kotu
  • Ana zargin dakataccen kwamishinan da mu'amala da wata matar aure, Tasleem Baba Nabegu wanda ya saba dokar musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta Kano ta bayyana lokacin da za ta gurfanar da dakataccen kwamishinan jihar Jigawa gaban kotu.

A karshen makon nan ne hukumar Hisbah ta kama Auwalu Danladi Sankara da zargin mu’amala da wata mata da ke da igiyar aure.

Kara karanta wannan

Kaico: Zargin aikata aikin assha da matar aure ya sa an dakatar da kwamishina a Jigawa

Sankara
Kotu za ta zauna ka zargin Sankara da mu'amala da matar aure ranar Talata Hoto: @Abusarki1
Asali: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa babban daraktan hukumar Hisbah, Malam Abba Sufi ne ya tabbatar da ranar gurfanar da dakataccen kwamishinan a kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hisbah: Za a kai dakataccen kwamishina kotu

Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, Kano ta sanya ranar Talata 21 Oktoba, 2024 don sauraron shari'ar dakataccen kwamishinan Jigawa.

Solacebase ta wallafa cewa za a fara sauraren karar da hukumar Hisbah ta shigar ta na tuhumar Auwalu Danladi Sankara da Taslem Baba Nabegu da mu'amala da juna.

Yadda Hisbah ta kama dakataccen Kwamishina

Hukumar Hisbah ta cafke Auwalu Danladi Sankara bayan mijin Tasleem ya shigar da kara hukumomi a Kano ya na zarginsu da aikata badala.

A yanzu dai Mai Shari'a Ustaz Ibrahim Sarki Yola zai fara sauraron shari'ar a ranar Talata bisa zarge-zargen da Hisbah ke yi wa mutanen biyu.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman abubuwa 5 game da kwamishinan da aka kama da zargin lalata da matar aure

An dakatar da kwamishina kan zargin lalata

A baya mun wallafa cewa gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Umar Namadi ta dakatar da kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Danladi Sankara.

Ana zargin kwamishinan da badala da matar aure bayan jami'an hukumar Hisbah a Kano sun kama shi da matar mai suna Tasleem Baba Nabegu a wani kango.

Tuni gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da kwamishinan, tare da kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.