Ministan Tinubu Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Rikicin Manoma da Makiyaya
- Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya nuna takaicinsa kan rikicin manoma da makiyaya a jihar Plateau
- Muhammad Badaru ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta samu ta kawo ƙarshen rikice-rikicen
- Ministan a buƙaci mutanen yankunan da ke fama da wannan matsala da su haƙura su zauna lafiya da juna a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana aniyar gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a jihar Plateau.
Ministan ya bayyana takaicinsa cewa duk da ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro suke yi na ganin an shawo kan rikicin, wasu ɓata gari na ƙoƙarin haddasa fitina.
An yi zama saboda rikicin makiyaya da manoma
Badaru ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin wani taron sasantawa da masu ruwa da tsaki a birnin Jos na jihar Plateau, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya kasance tsakanin shugabanni, sarakunan gargajiya da malaman addini daga ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos, Mangu da Riyom na jihar.
Ministan tsaro ya magantu kan rikicin makiyaya
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta damu matuƙa da yadda wasu ke son kawo cikas ga noman da ake yi a halin yanzu, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya kuma bayyana cewa kiran da ake yi na raba al’ummomi bisa ga tsarin ƙabilanci da addini a matsayin abin da zai haifar da tashin hankali nan gaba.
"Gwamnatin tarayya ba za ta yarda da irin wannan buƙatar ba da za ta iya haifar da rarrabuwar kawuna da rashin jituwa a tsakanin ƴan Najeriya. Don haka zama tare ba zaɓi ba ne, wajibi ne."
"Wannan a bayyane yake kan yadda shugaban ƙasa ya tsaya tsayin daka wajen yaƙi da masu son ɓallewa a kowane ɓangare na ƙasar nan."
- Mohammed Badaru Abubakar
Ministan ya buƙaci mutanen yankunan da su ƙauracewa tashe-tashen hankula, su rungumi zaman lafiya domin tabbatar da ci gaban tattalin arziƙin ƙasar nan.
An farmaki makiyaya a jihar Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙingiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana yadda wasu miyagun mutane su ka kai wa Fulani makiyaya farmaki a jihar Plateau.
Shugaban ƙungiyar, Babayo Yusuf ne ya tabbatar da hare-haren, ya ce an kashe wasu Fulani a lokacin da su ke kiwo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng