Tinubu Ya Shiga Ofis bayan Hutu, Talakawa Sun Tura Masa Bukatu

Tinubu Ya Shiga Ofis bayan Hutu, Talakawa Sun Tura Masa Bukatu

  • Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa kan halin da ake ciki bayan dawowar shugaba Bola Ahmed Tinubu daga hutu daga ketare
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ya iso Najeriya bayan ya shafe mako biyu cikin hutu na musamman Birtaniya da Faransa
  • Yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta sun yi martani da ganin shugaban kasar zaune cikin ofis a safiyar ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara aiki daga dawowarsa daga hutun mako biyu daga ketare.

Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun yi martani kan shiga ofis da shugaban kasar ya yi a farko bayan dawowarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi wanda ke ba shi shawara tun bayan hawansa mulki, ya yaba masa

Tinubu
Tinubu ya shiga ofis bayan dawowa daga hutu. Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hadimin Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya shiga ofis bayan hutu

A safiyar yau Litinin, 21 ga watan Oktoba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara shiga ofis bayan dawowarsa daga hutu.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Bola Tinubu ya fara tunkarar ayyuka a Aso Rock Villa a safiyar yau domin nausa ƙasa gaba.

Yan Najeriya suna zuba ido domin ganin yadda shugaban kasar zai tunkari matsalolin da ya samu bayan tafiyarsa hutu.

Bukatun talakawa bayan dawowar Tinubu

Wani mai amfani da kafar Facebook, Umar Ibrahim Umar ya wallafa cewa Allah ya sa wannan fara aikin na Tinubu ya sa suga canji ta bangaren wutar lantarki da sauran matsalolin da ya kawowa kasar da kuma wanda ya tarar da su.

Kara karanta wannan

Bayan shafe makonni 2, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dawo Najeriya

A daya bangaren, Yusuf Sawaba ya bukaci a sanar da shugaban kasar cewa kungiyar malaman jami'a ta ASUU na shirin tsunduma yajin aiki a Najeriya.

A na shi ra'ayin, Hayatu Abdullahi Jibia cewa ya yi a yankinsu ana fama da rikici saboda harin da yan bindiga suka kai musu a ranar Laraba saboda haka suna bukatar dauki.

Tinubu zai tura kudi ga talakawa ta banki

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai fara turawa talakawan Najeriya kudi ta asusun banki domin rage radadin rayuwa.

A bisa sanarwar gwamnatin tarayya, talakawa miliyan 20 ne za su ci moriyar shirin a fadin Najeriya idan aka fara nan gaba kadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng