Kama Yan Bindiga Ya Sanya Fara Sakin Fursunoni a Zamfara, Bayanai Sun Fito

Kama Yan Bindiga Ya Sanya Fara Sakin Fursunoni a Zamfara, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ziyarci gidan gyara halin Gusau domin fitar da wadanda suke daure saboda laifuffuka
  • Gwamnatin Zamfara ta bayyana dalilan da suka sanya gwamnan yin afuwa ga fursunonin da kuma yadda aka zakulo su daga kurkukun
  • Har ila yau, gwamna Dauda Lawal ya yi kyauta mai gwaɓi ga dukkan fursunonin da kuma yi musu kira na musamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta yi afuwa ga wasu fursunoni da ke gidan gyaran hali na Gusau.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa dole a saka ido ga kurkuku musamman yadda ake kara kama yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Dauda
An saki fursunoni a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Zamfara ya yi afuwa ga fursunoni

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi afuwa ga fursunoni 31 da ake kulle da su a gidan gyaran hali na Gusau.

Mai girma Dauda Lawal ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar yin afuwa ga fursunoni.

Dalilin sake fursunoni a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa a yanzu haka ana kama yan bindiga da dama a jihar kuma ana kai su kurkuku.

Saboda haka ya ce dole a rika daukar matakin rage cunkoso kuma hakan ne ya saka shi yin afuwa ga fursunonin su 31.

Gwamna ya yi kyauta ga fursunoni

Biyo bayan sakin fursunonin, gwamna Dauda Lawal ya ba kowane ɗaya daga cikinsu kyautar kuɗi N50,000.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 da ake zargi da rushe kadarori a jihohinsu kan bambancin siyasa

Gwamnan ya ce kudin zai taimaka musu wajen rage raɗaɗi idan suka koma cikin al'umma da zama.

Shugaban gidan yarin Gusau, Dr Umar Galadima ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa kokarin da ya yi.

Tinubu zai tura kudi ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu za ta fara tura kudi ga talakawan Najeriya ta asusun banki.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka yayin wani taro inda ya ce gwamnati za ta raba kudin ne domin rage radadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng