Bankin Duniya Ya Tono Wata 'Barna' da aka yi a Gwamnatin Buhari

Bankin Duniya Ya Tono Wata 'Barna' da aka yi a Gwamnatin Buhari

  • Bankin duniya ya yi sharhi kan yadda harkokin kuɗi da tattalin arziki suka gudana a lokacin mulkin shugaba Muhammadu Buhari
  • Rahotanni sun nuna bankin ya bayyana cewa an samu koma baya ta bangaren tattalin arziki a shekaru takwas da Buhari ya yi a Najeriya
  • Haka zalika bankin ya yi yabo ga tsare tsaren gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin Najeriya ya fara habaka yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bankin duniya ya fitar da rahoto kan yadda tattalin arzikin Najeriya ke habaka bayan samun koma baya a cikin shekaru.

Bankin duniya ya ce an samu koma bayan haɓakar tattalin arziki a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

Buhari
Bankin duniya ya yi magana kan mulkin Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Jaridar the Guardian ta wallafa cewa bankin ya ce a yanzu haka Najeriya ta fara farfaɗowa bayan wasu matakai da gwamnati ke dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin duniya ya tono barnar Buhari

Bankin duniya ya bayyana cewa daga 1999 zuwa 2014 shugabannin Najeriya sun yi kokarin habaka tattalin kasar.

Bankin ya ce tun hawan Muhammadu Buhari a 2015 aka fara samun koma baya saboda wasu matakan tattalin arziki da ya dauka.

A lokacin da Najeriya ta ke samun koma baya a karkashin Buhari, bankin ya ce sauran kasashe sun cigaba ta ɓangaren tattalin arziki.

Bankin duniya ya yabi Bola Tinubu

A daya bangaren, bankin duniya ya yabi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa yadda yake gudanar da mulki a Najeriya.

Bankin ya ce tattalin Najeriya ya fara farfaɗowa tun bayan wasu matakan tattalin arziki da Bola Ahmed Tinubu ya dauka.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan maido tallafin man fetur

A cewar bankin, duk da za a sha wahala a karon farko, amma ko a yanzu haka tsare tsaren Bola Tinubu sun fara haɓaka tattalin Najeriya.

Tallafin mai: Bankin duniya ya yi magana

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa bankin duniya ya buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da rike tsare tsarensa.

Bankin duniya ya gargadi shugaba Tinubu kan cewa idan ya dawo da tallafin mai Najeriya za ta shiga cikin bala'in rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng