Ziyarar Farko: Sarki Sanusi II Ya Fito da Wasu Bayanai yayin Ta'aziyya a Jigawa
- Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi wasu bayanai masu muhimmanci yayin ziyarar ta'aziyya a Jigawa
- Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara Jigawa ne domin yin jaje ga al'ummar jihar bayan mummunan hadarin tankar mai
- Sarkin ya bayyana irin yadda gwamna Umar Namadi ke samun yabo kan wasu ayyukan cigaba da yake kawowa jihar Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar jaje jihar Jigawa bayan hadarin tankar man fetur.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa gwamna Umar Namadi yana shan yabo kan kokarin da yake yi na kawo cigaba a jihar Jigawa.
Legit ta tatttaro bayanan da Sanusi II ya yi ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Umar Namadi, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi ya yi jaje a jihar Jigawa
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya isa birnin Dutse na jihar Jigawa domin yin jaje bayan haɗarin tankar mai.
Sanusi ya yi addu'ar samun gafara ga wadanda tsautsayin ya ritsa da su inda ya ce Allah yasa sun yi shahada.
Ya kuma roki Allah ya ba shugabanni ikon cigaba da kawo canji a Najeriya musamman lura da halin da ake ciki a yau.
Ziyar Sanusi II ta farko a Jigawa
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ziyarar ce ta farko da ya yi a fadar gwamnatin jihar Jigawa.
Ya kuma bayyana cewa Kano da Jigawa abu daya ne a wajensu sannan ya yi fatan cigaba da karfafa alaka tsakanin jihohin.
Ƙoƙarin gwamnan Jigawa, Umar Namadi
Sarki Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa gwamna Umar Namadi na matukar ƙoƙari a jihar Jigawa.
Ya ce wata rana yana tattaunawa da Jakadan Najeriya a Birtaniya yake ce masa ayyukan da suke yi tare da gwamna Namadi suna da matuƙar kyau.
Abba ya ba da tallafin N100m a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta mika tallafin N100m ga wadanda suka shiga tsautsayi yayin hadarin mota a jihar Jigawa.
A makon da ya wuce Abba Kabir Yusuf ya taka zuwa jihar Jigawa domin mika tallafin kuma shi ne gwamna na farko da ya yi hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng