"Ka da Ku Tsaya a Baya": Gwamna Ya Fito Ya ba Matasan Najeriya Muhimmiyar Shawara

"Ka da Ku Tsaya a Baya": Gwamna Ya Fito Ya ba Matasan Najeriya Muhimmiyar Shawara

  • Mai girma Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya kwadaitar da matasan Najeriya alherin da ke cikin samun madafun iko
  • Otti ya buƙaci matasa da su shiga harkokin siyasa domin samun damar yanke shawara kan abin da ya shafi rayuwarsu
  • Gwamnan ya ce akwai sauye-sauye masu yawa da za su iya kawowa idan suka samu mulki waɗanda za su amfani mutanensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ba matasan Najeriya shawara kan su shiga cikin harkokin siyasa.

Gwamna Alex Otti ya buƙaci matasan Najeriya da su shiga harkokin siyasa domin yanke shawara kan makomarsu da kuma kawo sauyi.

Gwamna Otti ya ba matasan Najeriya shawara
Gwamna Otti ya bukaci matasa su shiga siyasa Hoto: Alex C. Otti
Asali: Facebook

Gwamna Otti ya ba da shawarar ne a lokacin ibada a cocin The Transforming Church a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kowace al’umma na buƙatar shugabancin da ya dace da ita, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Wace shawara Gwamna Otti ya ba matasa?

Gwamna Otti ya bayyana cewa Allah ne yake ba da mulki sannan ya shawarci matasa da su guji yin baya-baya da neman samun madafun iko.

"Idan ka zauna ka ce siyasa ta ƴan siyasa ce, to ƴan siyasa ne za su yanke maka komai."
"Ina ƙalubalantar dukkan matasa a nan. Ka da ku guje wa siyasa. A nan ne ake yanke shawara game da makomarku."
"Za ka iya yin sauye-sauye masu yawa idan kana da mulki, wannan shi ne damar da siyasa ke ba da wa ta kawo sauyin da kake son gani a rayuwar mutanenka."
"Hakan na faruwa ne saboda samun kujerar siyasa na ba mutane damar kawo sauyi ga rayuwar mutane masu yawa fiye da yadda ake tunani."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wa ƴan Najeriya albashir da ASUU ke shirin rufe jami'o'i

- Gwamna Alex Otti

Gwamna Otti zai fara biyan N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Abia ƙarƙashin jagorancin Alex Otti ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi daga watan Oktoba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Okey Kanu ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Satumba yayin da yake zantawa da manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng