'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a garin Jibia
  • Ƴan sandan tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun kuma ceto mutane shida da ƴan bindigan suka sace
  • Ƴan sandan sun yi fatattakar miyagun ne bayan sun samu kiran gaggawa kan harin da suka kawo a garin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta yi nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai.

Ƴan sandan sun kuma kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a Unguwar Batsaka a cikin garin Jibia.

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan an hallaka jami'in dan sanda har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an samu kiran gaggawa a ofishin ƴan sanda na Jibia dangane da wasu ƴan bindiga da suka kai hari Unguwar Batsaka. 

An bayyana cewa maharan na ɗauke da muggan makamai inda suka riƙa yin harbi ba kakkautawa a lokacin da suke yunƙurin sace mutane a unguwar.

Ƴan sanda sun fatattaki ƴan bindiga

"A gaggauce DPO na Jibia ya haɗa tawagar jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar sojoji, jami'an rundunar KSCWC, da kuma ƴan banga zuwa wajen da lamarin ya faru."
"Sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan har na kusan sa'a ɗaya inda suka tilastawa ƴan bindigan tserewa daga wurin ɗauke da raunuka daban-daban."
"Tawagar ta yi nasarar ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, inda nan take aka garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu saboda raunukan da suka samu sakamakon harin da ƴan bindigan suka kai."

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda, sun kwato makamai masu yawa

"Abin takaici ɗaya daga cikin mutanen mai suna Rabe Mai Shayi, ya rasu a lokacin da yake karɓar magani."

- ASP Abubakar Sadiq Aliyu

Ƴan bindiga na kai hare-hare a Jibia

Mataimakin shugaban kwamitin tsaro na Jibia, Malam Nasiru Jibia ya shaidawa Legit Hausa cewa a cikin ƴan kwanakin ƴan bindiga na shigowa garin.

Ya bayyana cewa a cikin satinnan ƴan bindiga sun shigo garin har sau biyu.

"A cikin satinnan sau biyu suna shigo cikin gari. Lamarin sai addu'a amma jami'an tsaro na yin ƙoƙari sosai idan muka kira su."

- Malam Nasiru Jibia

Ƴan sanda sun cafke masu zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka yi dandazo a kan titin Lekki a jihar Legas.

Masu zanga-zangar sun taru ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba 2024, domin tunawa da 'zaluncin' da suka ce jami'an tsaro sun yi wanda ya yi ajalin matasa a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng