'Ta Dawo Makabarta': Obasanjo Ya Fadi Dalilin Rashin Samun Cigaba a Najeriya

'Ta Dawo Makabarta': Obasanjo Ya Fadi Dalilin Rashin Samun Cigaba a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki shugabanni kan rashin aiwatar da tsare-tsaren da suka kawo
  • Obasanjo ya ce ba a rasa tsare-tsare masu kyau ba a kasar illa kawai rashin aiwatar da su a aikace da watsi da su
  • Tsohon shugaban ya bayyana takaici yadda ake lalata tsare-tsare masu kyau a Najeriya inda ya ce kasar ta yi hannun riga da cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fadi abin da ke hana Najeriya samun cigaba.

Obasanjo ya ce dole Najeriya ta dauki matakan gyara ko kuma ta cigaba da sabani da abubuwan cigaba.

Kara karanta wannan

Bayan shafe makonni 2, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dawo Najeriya

Obasanjo ya caccaki shugabannin Najeriya kan tsare-tsare
Olusegun Obasanjo ya ba da shawara kan tsare-tsaren shugabanni a Najeriya. Hoto: Olusegun Obasanjo.
Asali: Getty Images

Olusegun Obasanjo ya soki tsare-tsaren shugabannin Najeriya

Obasanjo ya fadi haka ne a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024 a Abuja yayin wani babban taro, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ba ta rasa tsare-tsare ba da za su kawo cigaba illa rashin ba su kulawa kawai.

Ya koka kan yadda Najeriya ta zama makabarta da ke binne tsare-tsare masu kyau wadanda za su kawo sauyi, cewar rahoton Daily Post.

Olusegun Obasanjo ya ba shugabannin Najeriya shawara

"Bai kamata shugabanni suna yin magana ko kuma kawo tsare-tsare ba babu aikatawa."
"Ba mu rasa tsare-tsare a Najeriya ba kawai ta dawo makabarta na binne su ne saboda babu amfani ko aiwatarwa."
"Waɗanda suka cigaba sun yi ne ta hanyar aikatawa ba magana kadai ba, babu cigaba a kasar da ke gaba ta dawo baya."

Kara karanta wannan

"Na cancanta," Sanatan APC ya bayyana shirinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya fadi halin da Najeriya ke ciki

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan halin wahalar rayuwa da talakawa ke ciki a fadin Najeriya.

Cif Olusegun Obasanjo ya dura kan shugabanni yana mai cewa Allah ya samar da abubuwan da za a saka talaka ya ji dadin rayuwa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana rawar da dukkan yan Najeriya za su taka wajen ganin an ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.