Bayan Ya Dawo Najeriya, Tinubu Ya Sake Tura Shettima Wajen Wani Taro
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen taron shugabannin ƙasashe rainon Ingila (CHOGM) na shekarar 2024
- Mataimakin shugaban ƙasan zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa wajen taron wanda za a gudanar a ranakun 21 zuwa 26 ga watan Oktoban 2024
- Shettima zai yi amfani da taron wajen jawo masu zuba hannun jari ƴan ƙasashen waje zuwa Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen taron CHOGM.
Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa wajen taron shugabannin ƙasashe rainon Ingila (CHOGM) na shekarar 2024
Shettima zai wakilci Tinubu a wajen taro
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Stanley Nkwocha ya bayyana cewa Kashim Shettima zai haɗu da Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin duniya daga ƙasashe mambobi 56 a taron CHOGM.
Yaushe za a yi taron CHOGM?
Za a gudanar da taron na CHOGM wanda shi ne karo na farko a tsibirin Apia a Samoa daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Oktoba.
A wajen taron, Najeriya da sauran ƙasashe mambobi za su zaɓi sakatare janar na ƙungiyar Commonwealth na gaba.
Sabon sakatare janar ɗin da za a zaɓa zai fito ne daga yankin Afirika, sannan ƙasashen Lesotho, Ghana da Gambia ne za su nemi kujerar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shettima zai yi amfani da taron wajen jawo masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.
Tsohon SSG ya ba ƴan Najeriya shawara kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Ogun, Taiwo Adeoluwa, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnatin Bola Tinubu kan wahalhalun da ake sha sakamakon manufofin gyara tattalin arziƙi da ta kawo.
Adeoluwa ya jaddada cewa ya kamata ƴan Najeriya su yi haƙuri, kuma su kalli wannan lokaci mai cike da ƙalubale a matsayin sadaukarwar da ta dace domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng