Tsohon SSG Ya Fadi Abin ya Dace 'yan Najeriya Su Yi Wa Tinubu kan Tsadar Rayuwa

Tsohon SSG Ya Fadi Abin ya Dace 'yan Najeriya Su Yi Wa Tinubu kan Tsadar Rayuwa

  • Tsohon sakataren gwamnatin jihar Ogun ya yi magana kan matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan
  • Taiwo Adeoluwa ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu a ƙoƙarin da take yi na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan
  • Ya ƙara nan ba da jimawa ba za a amfana da manufofin gyara tattalin arziƙi da Bola Tinubu ya kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Ogun, Taiwo Adeoluwa, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnatin Bola Tinubu kan wahalhalun da ake sha sakamakon manufofin gyara tattalin arziƙi da ta kawo.

Adeoluwa ya jaddada cewa ya kamata ƴan Najeriya su yi haƙuri, kuma su kalli wannan lokaci mai cike da ƙalubale a matsayin sadaukarwar da ta dace domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su daina korafi, ya ba su shawara

Tsohon SSG ya ba 'yan Najeriya shawara
Tsohon SSG na Ogun ya bukaci a kara hakuri da Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Adeoluwa ya ce duk da cewa abubuwa sun yi tsauri ga ƴan Najeriya a yanzu, wannan ba yana nufin gwamnati ba ta kan hanya mai kyau ba, cewar rahoton jaridar The Punch

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon SSG ya ba da shawara

Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ƴan Najeriya za su fara cin gajiyar waɗannan sauye-sauyen da ake aiwatarwa domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

"Babu shakka cewa mutane suna shan wuya. Abin da ya sa lamarin ya zama ruwan dare shi ne kowa ya damu, amma zan iya gaya muku kyauta cewa wannan gwamnatin tana kan hanyar da ta dace."
"A matsayinmu na ƴan Najeriya, dole ne mu yi haƙuri kafin mu fara cin gajiyar waɗannan sauye-sauyen. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne, kuma muna yi wa Shugaba Bola Tinubu fatan alheri kan duk abin da ya sa a gaba."

Kara karanta wannan

Zababben gwamna ya bankado badakalar da ake shiryawa kafin a mika masa mulki

- Taiwo Adeoluwa

Gwamnatin Tinubu za ta ƙaƙaba haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta shirya kakaba harajin kashi biyar kan kiran waya, data da sauran ayyukan sadarwa, wasanni, caca da sauransu.

Bullo da sabon harajin na daga cikin wani bangare na sabon kudirin dokar da gwamnatin za ta gabatar na yin garambawul ga tsarin harajin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng