Gwamna a Arewa Ya Shiga Layi, Ya Sanar da Sabon Albashin da Zai Iya Biyan Ma'aikata
- Ma'aikatan gwamnati a jihar Kwara za su fara cin moriyar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 daga watan Oktoba, 2024
- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya umarci a fara biyan sabon al.bashin nan take bayan ganawa da ƴan kwadago da kamfanoni
- Kwamishinar kuɗi ta jihar Kwara, Dr. Hauwa Nuru ta ce wannan mataki ya kara nuna yadda gwamna ya himmatu wajen inganta walwalar ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara - Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya bi sahun wasu gwamnoni a shirin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamna Abdulrazaq ya ba da umarnin a fara biyan ma'aikatan jihar Kwara sabon albashin daga wannan watan da muke ciki watau Oktoba, 2024.
Kwamishinar kuɗi, Dr Hauwa Nuru ce ta bayyana haka a wata sanarwa da gwamnatin Kwara ta wallafa a shafin X ranar Asabaar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kwara ya amince da N70,000
Dr Hauwa ta ce gwamnan ya amince da N70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci kamar yadda gwamnatin tarayya ta cimma matsaya da ƴan kwadago.
Hauwa Nuru ta ce:
"A wani yunkuri na inganta jin dadin ma’aikata a Kwara, Mai girma gwamna Malam AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 kamar yadda gwamnatin tarayya ta sanar.”
Yaushe za a fara biyan sabon albashi a Kwara?
Kwamishinar ta bayyana cewa za a aiwatar da wannan doka ta mafi ƙarancin albashi a watan Oktoba, ma'ana za a fara biyan ma'aikata a wannan wata.
A cewarta, an cimma wannan matsaya ne a wani taro da aka yi tsakanin gwamnatin Kwara, ƴan kwadago NLC, TUC da kamfanoni masu zaman kansu.
Hauwa Nuru ta yabawa Gwamna AbdulRazaq bisa baiwa kwamitin da aka kafa cikakken ‘yanci har aka cimma matsayar da za ta amfanar da dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Ta ƙara da cewa mai girma gwamna ya himmatu wajen kyautata rayuwar ma'aikata da ɗaukacin al'ummar jihar Kwara.
Wata ma'aikaciya a Kwara, Malama Khadija Sani ta shaidawa wakilin Legit Hausa cewa hakan abin a yabawa gwamna ne amma fa ba abin da N70,000 za ta wa ma'aikaci.
A cewarta, duba da halin tsadar rayuwa da rashin tabbas a farashin muhimman kayayyaki, wannan ƙarin albashi ba zai rage komai.
"Ina mamakin taya ma'aikaci mai iyali zai rayu a wata da N70,000? Muna cikin wani hali a ƙasar nan ta yadda ba za ka iya cewa ga farashin abu ba, k saya yau gobe a ce maka ya tashi.
"Muna kira ga gwamnati bayan ta fara biyan sabon albashin ta kuma duba yiwuwar ƙayyade farashin kayayyaki musamman na abinci," in ji ta.
Gwamna Fubara ya kara albashi zuwa N85,000
A wani rahoton kuma Gwamna Siminalayi Fubara ya kere N70,000, ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Ribas.
Shugaban ma'aikatan jihar, George Nwaeke ya ce gwamnan ya amince da sabon albashin ne yayin ganawa da ƴan kwadago.
Asali: Legit.ng