Tinubu Ya Fadi Wanda Ke ba Shi Shawara Tun Bayan Hawansa Mulki, Ya Yaba Masa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon murnar cika shekaru 90
- Tinubu ya bayyana irin gudunmawar da Gowon ya ba Najeriya lokacin mulkinsa inda ya ce ya yi matukar taka rawa
- Wannan na zuwa ne yayin dattijon ke bikin cika shekaru 90 a duniya inda manyan Najeriya da dama suka taya shi murna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yaba da rayuwar Janar Yakubu Gowon.
Tinubu ya fadi haka ne yayin taya tsohon shugaban kasa, Gowon murnan cika shekaru 90 a duniya.
Tinubu ya taya Gowon murnar cika shekaru 90
Tinubu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta wallafa a shafin X a jiya Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce Gowon ya kasance mai ba shi shawara tun bayan hawansa shugabancin Najeriya.
Shugaban ya yabawa Gowon duba da yadda ya mulki Najeriya da kuma gudunmawar da ya bayar na musamman.
Tinubu ya yabawa Janar Yakubu Gowon
"Tun bayan hawa na kan shugabancin Najeriya, Gowon ya kasance yana ba ni shawarwari kan abubuwa da yawa idan bukatar hakan ya tashi."
"Gowon ya kasance tare da mu lokacin da muka samu sabani da makwabtanmu ƙasashe, inda ya bukaci gyara alaka saboda kungiyar ECOWAS."
"Bayan gudunmawar da ya bayar a ofis, Gowon yana cigaba da kasancewa dattijo tare da nuna muhimmancin shekaru."
- Bola Tinubu
Tinubu ya ce Gowon ya kasance yana addu'o'i ga Najeriya tare koyar da zaman lafiya musamman a tsakanin addinai guda biyu.
An fadi yadda Tinubu ke yawo da dare
Kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya yi albishir ga yan kasar nan kan samun saukin matsin rayuwa da tsadar kayan amfanin yau da gobe.
Sanatan mai wakiltar Abia ya ce shugaban kasa kan yi rangadi lokaci zuwa lokaci domin ganewa idanunsa halin da ake ciki.
Ya kara da cewa ba kasar nan kawai ke fama da talauci da kuncin rayuwa ba, sauran kasashe na fama da irin matsalolin.
Asali: Legit.ng