Kaico: Zargin Aikata Aikin Assha da Matar Aure Ya Sa an Dakatar da Kwamishina a Jigawa

Kaico: Zargin Aikata Aikin Assha da Matar Aure Ya Sa an Dakatar da Kwamishina a Jigawa

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana dakatar da kwamishinan da aka zarga da lalata da matar aure a wani yankin jihar Kano
  • A baya, hukumar Hisba ta kama kwamishinan jihar Jigawa a wani kango a Kano tare da wata matar da ake zargin matar aure ce
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi da tofa albarkacin baki a Arewa kan zargin da ake yiwa kwamishinan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya dakatar da kwamishinansa na ayyuka na musamman, Auwalu Sankara, har sai an gudanar da bincike kan zargin da hukumar Hisbah ta jihar Kano ke yi a kansa.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama Sankara, a wani gini da ba a kammala ba tare da wata matar aure tare da zarginsa da aikata lalata.

Kara karanta wannan

Kano: Ana so a raba shi da Kwankwaso, Gwamna Abba ya amince da ayyukan N36bn

An dakatar da kwamishinan ayyuka na Jigawa daga aiki
Yadda aka dakatar da kwamishinan ayyuka na Jigawa kan zargin lalata | Hoto: Jigawa State Government, Nigeria
Asali: Facebook

Darakta Janar na hukumar, Dakta Abba Sufi, ya tabbatar da kama Sankara tare da matar a yammacin ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba.

Abin da gwamnati ke fadi

A wata sanarwar da kwamishinan ya fitar a daren Juma’a, ya ce Sankara ya musanta zargin, inda yace karya aka masa, maras tushe, kuma kage.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi ikirarin zargin wani yunkuri ne na bata masa suna da gangan daga wadanda ke adawa dashi.

Sai dai a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim a ranar Asabar ta bayyana cewa an dakatar da kwamishinan.

Hakazalika, gwamnatin ta bayyana cewa, za ta jira har sai an gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya ko akasin haka.

Gwamnati ta nada kwamitin bincike kan kwamishina

Kara karanta wannan

Sankara: Kwamishina ya magantu kan zarginsa da Hisbah ke yi, ya fadi matakin gaba

A bangare guda, gwamnatin jihar ta kuma nada kwamitin bincike don tabbatar da abin da ke faruwa da kwamishina Sankara.

Malam Bala Ibrahim, sakataren gwamnatin jihar ne zai jagoranci kwamitin tare da wasu manyan jami’an gwamnati hudu.

Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da zargin ba, kuma gwamnati ta ce za ta bincika kafin daukar matakin karshe.

Martanin kwamishina Sankara kan zargin da ake masa

A tun farkon fitan zargin, kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa ya yi magana kan zargin da ake yi masa.

Auwal Danladi Sankara ya musanta labarin cewa an kama shi yana lalata da matar aure a jihar Kano.

Legit Hausa ta baku labarin yadda Hukumar Hisbah ta kama kwamishinan a cikin wani kango.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.