Alaƙa Ta Kara Tsami Tsakanin Gwamna da Babban Basarake, Sarkin Ya Tura Masa Sako

Alaƙa Ta Kara Tsami Tsakanin Gwamna da Babban Basarake, Sarkin Ya Tura Masa Sako

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa alaka ta kara tsami tsakanin Gwamna Charles Soludo da Igwe Alfred Achebe na Onitsha
  • Gwamnan ya kauracewa bikin Ofala na gargajiya da ake yi kowace shekara a Onitsha saboda bunkasa al'adu
  • Hakan bai rasa nasaba da dakatar da Obi na Neni da ya ba abokin hamayyarsa, marigayi Sanata Ifeanyi Ubah sarauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Alaka na kara tsami tsakanin Gwamna Charles Soludo da Obi na Onisha a jihar Anambra.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan bai halarci taron gargajiya ba saboda matsalar da ke tsakaninsu.

Gwamna ya sha suka kan rashin mutunta masarautun gargajiya
Gwamna Charles Soludo ya kauracewa bikin Ofala na gargajiya da ake yi a Onitsha. Hoto: Igwe Alfred Achebe, Prof. Charles Soludo.
Asali: Facebook

Gwamna Soludo ya kauracewa taron gargajiya

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya ƙara ƙamari, babban basarake a Arewa ya yi murabus daga sarauta

Daily Trust ta ce Soludo ya kauracewa taron gargajiya na da ake yi kowace shekara a jiya Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan bai rasa nasaba ta takun-saka da ke tsakanin Soludo da Igwe Alfred Achebe na birnin Onitsha a jihar.

A shekarar bara yayin bikin, Gwamna Soludo ya sha alwashin hada kai da basaraken domin bunkasa Ofala.

Sai dai komai ya lalace bayan Soludo ya dakatar da Igwe Ezeani na Neni bayan nada marigayi Sanata Ifeanyi Ubah sarauta.

Gwamnan na tsoron Ubah zai kawo masa barazana a kujerarsa da yake son nema kafin ya rasu a watan Satumbar 2024 da muke ciki.

Anambra: Sakon basaraken ga Gwamna Charles Soludo

Igwe Achebe ya ce kwata-kwata gwamnan bai mutunta masarautun gargajiya a jihar inda hakan ke kara kawo cikas ga cigaban al'adun jihar.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Basaraken ya ce kowace jiha a Najeriya na hada kai da masarautun gargajiya domin bunƙasa al'adu amma an bar Anambra a baya.

Gwamna zai zaftare kudin kananan hukumomi

Kun ji cewa Gwamnan Anambra ya kafa dokar rage wani kaso daga cikin kuɗin da Gwamnatin tarayya za ta rika turawa kananan hukumomin jihar.

Farfesa Charles Soludo ya ce yana ganin akwai matsala idan aka ba kananan hukumomi cikakken ikon cin gashin kansu.

Wannan na zuwa ne bayan kotun ƙoli ta yi hukuncin turawa kowace ƙaramar hukuma kudinta kai tsaye daga asusun Tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.