Zaune Bata Kare Ba: Tsageru Sun Ci Gaba da Ta’addanci a Arewa, Sun Tafka Barna a Katsina

Zaune Bata Kare Ba: Tsageru Sun Ci Gaba da Ta’addanci a Arewa, Sun Tafka Barna a Katsina

  • An samu wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a wani yankin jihar Kastina da ke Arewacin Najeriya
  • An yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da mata da yara yayin da wasu suka samu munanan raunuka
  • Jihohin Arewa maso Yamma na fuskantar sace-sace da farmkakin ‘yan ta’adda da ke cutar da al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Katsina - Wasu tsageru sun farmaki a kauyen Dan Auta da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina da sanyin safiyar Juma’a 18 ga watan Oktoba.

Farmakin da aka kai da misalin karfe 2 na safe, ya yi sanadin rasa mutane biyu ciki har da jami’in tsarin jiha KSCWC, tare da sace mutum 13 da suka hada da mata da kananan yara.

Daga cikin wadanda aka sace har da shugaban jam’iyyar APC mai mulki a yankin, mai suna Alhaji Imamu.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun kashe jami'in tsaro

An kai hari jihar Katsina, an sace mutane
Yadda aka kai hari jihar Katsina, garin gwamna Radda | Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya auku

Shaidu sun bayyana cewa, tsagerun sun isa wurin da yawan gaske, suna kan babura da dauke da muggan makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da kokarin da jami’an KSCWC da kungiyoyin ’yan banga na yankin suka yi na dakile harin, yawan maharan ya rinjayi rundunar tsaron yankin.

Rahoton jaridar Leadership ya ce, an rasa ma’aikacin KSCWC ne a lokacin da yake kokarin kare jama’a, yayin da aka ce an bindige na biyun bayan da ya ki amincewa da yunkurin sace shi.

Mutane sun samu raunuka

Wasu mazauna garin da dama sun samu raunuka a yayin harin, inda wasu ke karbar magani a cibiyar kula da lafiya a matakin farko na kauyen.

Wannan lamari dai ya kara nuna irin kalubalen tsaro da ake fama da shi a Jihar Katsina.

Jihohin Arewa maso Yamma, na ci gaba da fuskantar farmakin ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da barayin shanu.

Kara karanta wannan

Satar wayoyi 100 ta jefa wasu daliban Arewa a cikin matsala, 'yan sanda sun yi bayani

Masu aikata laifuka sukan yi amfani da wanzuwar dazuzzuka a jihar ta Katsina da jihohin makwabta a matsayin maboyarsu.

Wani farmakin na daban a Katsina

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan Sanusi Ango Gyaza, mai taimaka wa gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a Gyaza, da ke karamar hukumar Kankia.

Gyaza, wanda tsohon shugaban kungiyar malamai ta Najeriya NUT na karamar hukumar Kankia ne, an kashe shi a harin tare da matarsa kamar yadda rahoto ya nuna.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bakin kakakinta Abubakar Sadiq, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inji rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.