"Ba Za Ta Saɓu ba," Gwamna a Arewa Ya Ɗauki Zafi kan Sace Kuɗin Marayu N2.1bn
- Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ɗauki matakin dawo da kuɗaɗen marayu da wasu marasa imani suka sace
- Nasir Kauran Gwandu ya ce ba zai naɗe hannu yana kallo wasu tsiraru su zalunci marayu waɗanda ke kokarin kulawa da kansu ba
- Wata kungiyar Musulmai ta duniya ce ta rabawa marayu kusan 2,000 tallafin N2.1bn domin su ɗauki ɗawainiyar kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya nuna damuwa kan kwace wa wasu marayu kudaden da suka samu na tallafi daga kungiyar Musulmi ta duniya.
Gwamnan ya kafa kwamitin da zai gudanar da bincike domin dawo da kuɗaɗen da aka ɗaukewa marayun daga cikin Naira biliyan 2.1 da aka raba masu don su taimaki kansu.
Punch ta ruwaito cewa a ranar 10 ga watan Oktoba, kungiyar Musulmi ta duniya ta turawa marayu 1,849 tallafin N2.1bn ta asusun bankuna don su kula da kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu sun yaudari marayu a Kebbi
To sai dai abin mamakin sai hakan ya ba wasu daga cikin masu riƙe da marayu dama, inda suna riƙa karɓewa marayun kuɗaɗen ta hanyar damfara.
Wannan ya jawo hankalin Gwamma Nasir Idris, inda ya ba da umarnin a gaggauta karɓo waɗannan kudi a maidawa marayun, rahoton Daily Trust.
Kwamishinan harkokin addini, Alhaji Muhammad Sani-Aliyu ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai ranar Juma'a a Birnin Kebbi.
Gwamnatin Kebbi ta kafa kwamiti
Muhammadu Sani ya ce:
"Gwamna yana tausayin marayu kuma ba zai bar lamarin ya wuce sakaka ba, ya umarci kwamitin ya yi duk abin da ya kamata don tabbatar da gaskiya."
"Mun tuntuɓi bakunan da suka yi aikin rabawa marayun kudin kuma sun shaida mana an yi amfani da POS ne wajen kwashe kuɗin amma babu hannunsu.
"Duk da haka muna gargaɗin bankuna cewa duƙ wanda aka kama da cire kuɗin daga asusun marayu, gwamnati za ta rubuta takardar ƙorafi zuwa hekdwatar bankin."
Gwamna Nasir ya rabawa sarakuna motoci
A wani labarin kuma gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya bai wa sarakuna huɗu masu daraja ta farko manyan motoci.
Da yake miƙa masu mabuɗan motocin, gwamnan ya ce yana sane da rawar da suke takawa wajen samar da tsaro da ci gaba.
Asali: Legit.ng