An Shiga Jimami Bayan an Hallaka Jami'in Dan Sanda Har Lahira

An Shiga Jimami Bayan an Hallaka Jami'in Dan Sanda Har Lahira

  • Wani jami'in ɗan sanda da ba a bayyana sunansa ba ya rasa ransa a jihar Legas a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024
  • An hallaka jami'in ɗan sandan ne bayan ya jagoranci tawagarsa zuwa wani wajen da aka yi hatsari wanda ya jawo asarar ran wani ɗan Achaɓa
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ana ci gaba da farautar masu hannu a kisan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - An kashe wani jami'in ɗan sanda mai muƙamin ASP wanda ba a bayyana sunansa ba a jihar Legas.

Lamarin kisan ɗan sandan dai ya faru ne a unguwar Agege da ke jihar a safiyar ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Wani babban ɗan sanda ya mutu cikin ofis, an faɗi abin da ya faru

An kashe dan sanda a Legas
An hallaka dan sanda har lahira a Legas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An kashe ɗan sanda a Legas

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin ƴan Achaba ne da hannu a kisan da aka yi wa ɗan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya jagoranci tawagar ƴan sanda zuwa wurin da wani hatsari ya faru a mahaɗar WEMCO da ke kan titin Mobil, Agege, a lokacin da tawagarsa ta fuskanci mummunan hari.

An tattaro cewa ƴan sandan sun je ɗauke wata babbar mota ce da ta buge wani ɗan Achaba, amma sun gamu da turjiya daga ƴan Achaɓan da ke wajen inda suka dage cewa sai sun ƙona motar.

Me ƴan sanda suka ce?

Kakakin rundunar ƴan sandan jiihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana kisan a matsayin abin da bai dace ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa ASP ɗin mai shekara 46 ya rasu ne nan take a wajen bayan ya samu rauni a kansa.

Kara karanta wannan

Magidanci a Kano ya shiga matsala bayan ya raunata matarsa a wuri mai daraja

Ya ƙara da cewa an cafke mutane yayin da ake ci gaba da farautar sauran.

Ɗan sanda ya rasu a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƴan sandan wanda aka fi sani da DPO na caji ofis ɗin Ijanikin a jihar Legas, CSP Bolaji Olugbenga ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun nuna DPO ya yanke jiki ya faɗi ba zato ba tsammani a ofishinsa kuma rai ya yi halinsa tun kafin a kai ga zuwa asibiti ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng