Tsadar Rayuwa: Ministan Tinubu Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Daina Korafi, Ya Ba Su Shawara
- Ministan shari'a na Najeriya ya buƙaci ƴan Najeriya su daina ƙorafi kan halin matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar nan
- Lateef Fagbemi ya bayyana cewa kamata ya yi ƴan Najeriya su ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Ministan ya kuma yi gargaɗi ga masu kira ga sojoji da su karɓe mulki daga hannun farar hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Antoni Janar kuma ministan shari'a na Najeriya, Lateef Fagbemi, ya yi magana kan ƙalubalen tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar nan.
Ministan ya ce duk da ƙasar nan na fuskantar ƙalubale kafin zuwan Bola Tinubu, gwamnati mai ci ba zata tsame hannunta ba kan wuyar da ake sha a ƙasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wata lakca wajen taron yaye ɗaliban jami'ar Ilorin a jihar Kwara ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Tinubu ya ba ƴan Najeriya shawara
Lateef Fagbemi ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su daina ƙorafi kan halin da ake ciki a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa kamata ya yi su ci gaba da goyon bayan gwamnati mai ci domin cimma manufofinta na tsamo ƙasar nan daga halin da take ciki.
Ministan ya gargaɗi masu kira ga sojoji su karɓe mulki da su guji yin hakan, inda ya buƙaci masu son ganin manufofin Tinubu sun haifar da ɗa mai ido cikin sauri da su ƙara haƙuri su goyawa gwamnatin baya.
"Bai kamata mu bari ƙalubalen da ake fuskanta ba ya sa idanuwanmu su kulle kan amfanin mulkin dimokuraɗiyya. Wasu daga cikinmu da suka zauna a mulkin soja da dimokuraɗiyya sun san cewa bambancin a bayyane yake."
"Kamar dukkanin mutane masu tunani, ba mu fatan komawa lokacin mulkin soja."
- Lateef Fagbemi
Jigon APC ya koka kan mulkin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon APC, Joe Igbokwe ya nuna damuwa kan inda Najeriya ta dosa saboda ganin yadda abubuwa ke kara dagulewa a mulkin Bola Tinubu.
Mista Joe Igbokwe ya yi ishara da cewa halin da ake ciki a Najeriya na neman cire masa tsammanin samun sauki ko gyara.
Asali: Legit.ng