An Shiga Jimami a Majalisar Tarayya da Mutum 2 Suka Rasu cikin Awanni 24

An Shiga Jimami a Majalisar Tarayya da Mutum 2 Suka Rasu cikin Awanni 24

  • Wasu kwararrun ƴan jarida biyu da ke aiki a majalisar tarayya, Mr. Elijah Olaluyi da Malam Mohammed Adamu sun riga mu gidan gaskiya
  • Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi ta'aziyya ga iyalan ƴan jaridar tare da addu'ar Allah ya ba su haƙuri
  • Hon. Benjamin Kalu ya bi sahun Abbas wajen nuna alhinin wannan rashi da aka yi a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - An shiga jimami a majalisar tarayya yayin da wasu ƴan jarida biyu suka rasu cikin sa'o'i 24.

Shugaban majalisar wakailai, Rt. Hon Tajudeen Abbas ya yi ta'aziyyar rasuwar ƴan jaridar guda biyu a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Krishi ya fitar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya ƙara ƙamari, babban basarake a Arewa ya yi murabus daga sarauta

Majalisar wakilai.
Tajudeen Abbas ya yi ta'aziyyar rasuwar yan jarida 2 da ke aiki a majalisar tarayya Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Tajudeen Abbas ya aika saƙon ta'aziyya

A sanarwar Abbas ya miƙa sakon ta'aziyyar rasuwar Mr. Elijah Olaluyi, ɗan jarida mai ɗaukar hoto na jaridar Telegraph a majalisar tarayya, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma Tajudeen Abbas ya kuma yi ta'aziyyar rasuwar mai ɗaukar rahoto na gidan Radiyo da Talabijin na Liberty, Malam Mohammed Adamu.

Ƴan jarida 2 sun rasu cikin awanni 24

Olaluyi ya mutu ne da yammacin ranar Alhamis, yayin da Mohammedn Adamu, kwararren dan jarida ya rasu da sanyin safiyar Laraba.

Yayin da yake miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan Olaluyi da Mohammed, kakakin majalisar ya haɗa da yiwa gidajen jaridun da suke wakilta a majalisar ta'aziyya.

"Sun kasance ƙwararun ƴan jarida waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru suna aiki a majalisar tarayya kuma sun yi abubuwan da ba za a manta da su ba.

Kara karanta wannan

An barke da murna da kamfanin NNPCL da Chevron suka sake hako wata rijiyar mai

"Za mu yi kewarsu sosai, ina taya iyalansu da gidajen jaridun da suke wa aiki alhinin wannan rashi."

- Tajudeen Abbas.

Shugaban majalisar wakilan ya yi addu’ar Allah ya jikan su ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Benjamin Kalu ya bi sahun Abbas

Hakazalika, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Olaluyi, dan jarida mai daukar hoto a jaridar New Telegraph.

Kalu ya kuma mika ta’aziyya ga ‘yan jaridar majalisar dattawa bisa rasuwar Malam Mohammed Adamu, wakilin gidan rediyo da talabijin na Liberty.

DPO ya rasu a ofia a Legas

Kuna da labarin wani DPO na ƴan sanda a jihar Legas mai kula da caji ofis na Ijanikin, ya riga mu gidan gaskiya ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce CSP Bolaji Olugbenga ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi ba zato ba tsammani a ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262