Kano: Muhimman Abubuwa 5 Game da Kwamishinan da aka Kama da Zargin Lalata da Matar Aure

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Game da Kwamishinan da aka Kama da Zargin Lalata da Matar Aure

Dakarun hukumar Hisbah na Kano sun cafke kwamishinan ayyuka na musamnan a jihar Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara ranar Jumu'a, 18 ga watan Oktoba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan Hisbah sun damƙe kwamishinan ne bisa zargin lalata da wata matar aure a wani Kango a jihar Kano.

Auwal Sankara da Hisbah.
Yan Hisbah sun damke kwamishinan Jigawa, Auwal D Sankara a jihar Kano Hoto: @Abusarki1
Asali: UGC

Punch ta ruwaito cewa darakta janar na Hisbah, Abba Sufi ya ce jami'ai sun cafke Auwal Sankara dumu-dumu da matar aure a wani gini da ba a kammala ba.

Ya ce hukumar Hisbah ta samu wannan nasara ne ta hanyar bin diddigi bayan samun ƙorafe-ƙorafe kan ayyukan da kwamishinan ke yi a wurin.

"Eh gaskiya ne mun kama wani kwamishinan Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara tare da wata matar aure a wani kangon gini mallakinsa," in ji Sufi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya shirya ɗaukar sababbin ma'aikata sama da 17,000 a Kano, bayanai sun fito

Bayan haka ne Legit Hausa ta zaƙulo muku wasu mihimman bayanai game da kwamishinan wanda ya faɗa komar Hisbah a Kano.

1. Yaron ministan tsaro, Badaru

Bisa la'akari da wasu hotuna da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Auwal Sankara ya kasance ɗan siyasar gidan Mohammed Badaru Abubakar.

Badaru shi ne ministan tsaron Najeriya na yanzu kuma tsohon gwamna a jihar Jigawa. Haka nan ministan babban jigo ne a APC mai mulki.

2. Tsohon hadimin gwamna a Jigawa

Auwal Sankara ya yi aiki a matsayin babban mai taimakawa gwamna watau SSA a lokacin mulkin Badaru.

A Najeriya, ana naɗa SSA ne domin ya taimakawa shugaban kasa ko gwamna ko dai wani shugaba a wani ɓangare.

3. Shekara 2 da zama kwamishina

A watan Yulin 2022, Badaru ya naɗa Auwal Ɗanladi Sankara a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman.

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta tantance tare da tabbatar da naɗinsa a wannan lokaci, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta yi ram da kwamishina kan zargin lalata da matar aure

4. Ya yi aure a shekarar 2015

Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa kwamishinan ya yi aure a watan Afrilun 2015.

Sai dai har kawo yanzu ba a tabbatar da cewa matar na tare da shi har yau ko akasin haka ba.

5. Ɗan uwan ɗan takarar PDP

Bugu da ƙari Auwal Sankara ya kasance ɗan uwan tsohon ɗan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya a inuwar jam'iyyar PDP, Nafiu Ɗanladi Sankara.

Nafiu Ɗanladi dai ya kasance babban manajan darakta (MD) na kamfanin Sankara Nigeria Limited.

Za a ɗauki ma'aikata a Kano

A wani rahoton kuma gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gama shirye-shiryen ɗaukar jami'an tsaro 17,600 a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatn za ta ɗauki mafarauta aikin tsaro a wani ɓangare na kokarin bunƙasa harkokin ilimi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262