Kwana Ya Ƙare: Wani Babban Ɗan Sanda Ya Mutu cikin Ofis, An Faɗi Abin da Ya Faru
- Wani DPO na ƴan sanda a jihar Legas mai kula da caji ofis na Ijanikin, ya riga mu gidan gaskiya ranar Alhamis
- Rahotanni sun ce CSP Bolaji Olugbenga ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi ba zato ba tsammani a ofishinsa
- Har yanzu rundunar ƴan sanda ba ta ce uffan ba kan lamarin amma wani ɗan sanda ya fadi abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Shugaban ƴan sandan wanda aka fi sani da DPO na caji ofis ɗin Ijanikin a jihar Legas, CSP Bolaji Olugbenga ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun nuna DPO ya yanke jiki ya faɗi ba zato ba tsammani a ofishinsa kuma rai ya yi halinsa tun kafin a kai ga zuwa asibiti ranar Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa rasuwar babban ɗan sandan ta jefa jami'an caji ofis din cikin jimami da alhini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'dan sanda ya mutu a ofis
Wani dan sanda da ke aiki a caji ofis ɗin, wanda ya yi magana bisa sharadin a sakaya sunansa, ya ce an kai gawar wannanDPO zuwa dakin ajiyar gawa.
"Kwatsam ya yanke jiki ya faɗi ranar Alhamis kuma mun yi gaggawar kai shi asibiti amma abin takaici rai ya yi halinsa," in ji ɗan sandan.
Har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton rundunar ƴan sanda reshen jihar ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan rasuwar DPO ba.
Karanta wasu labaran ƴan sanda a Najeriya
- Rundunar ƴan sanda ta bude ƙofa, an fara karbar masu korafi kan jami'ai a Kano
- An kori yan sanda kan kitsa kashe dalibi yayin zanga zangar tsadar rayuwa
- Yan sanda sun farauto gawurtattun yan fashi da makami
IGP ya biya diyyar ƴan sandan Kano
A wani labarin kuma IGP Kayode Egbetokun ya ba da diyya ga iyalan ƴan sandan da suka rasu sakamakon hatsarin mota a jihar Kano.
Sufeto Janar na ƴan sandan ya ba da diyyar N10m ga iyalan waɗanda suka rasu tare da N2m ga jami'an da suke jinya a gadon asibiti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng