Yan Bindiga Sun Tunkari Abuja da Tsakar Rana, Sun Fafata da Yan Sanda
- Jami'an yan sandan Najeriya sun fafata da wasu miyagun yan bindiga da suka tunkari birnin tarayya Abuja da tsakar rana
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce jami'ai un kwato wasu daga cikin makaman miyagu yan bindigar
- An ruwaito cewa mutane ne suka yi gaggawar kiran yan sanda ta wayar tarho yayin da miyagun suka so yin ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta yi nasara kan wasu miyagu yan bindiga a birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yau Juma'a inda yan ta'addar suka nufi kai hari a Kubwa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa jami'an yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin kuma sun kwato motar miyagun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun tunkari Abuja da rana
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa a yau Jumu'a wasu yan bindiga a cikin mota suka tunkari Kubwa a birnin tarayya Abuja.
Bayan zuwan yan bindigar mutanen yankin suka gaggauta kiran yan sanda domin kawo musu dauki.
Yan sanda sun fatattaki yan bindiga
Rundunar yan sanda ta amsa kira da aka yi mata kuma jami'anta na zuwa wajen yan bindigar, suka fara bude wuta.
Nan take jami'an yan sanda suka fara mayar musu da wuta, da miyagun suka ga jami'an tsaro sun fi karfinsu sai suka fara gudu.
An kama dan bindiga a Abuja
A yayin da yan bindigar suka fara guduwa, jami'an yan sanda sun yi nasarar cafke daya daga cikinsu.
Kwamishinan yan sanda a Abuja ya tabbatar da cewa sun kwato bindiga ƙirar AK-47 guda daya, Pistol daya da kuma tarin harsashi.
The Guardian ta wallafa cewa CP Tunji Disu ya kuma tabbatar da cewa sun yi nasarar kwace wata mota da miyagun suka zo da ita.
An kama gidan da ake ajiyar makamai
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke wasu mutane da ke ajiyar makamai ga yan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa cikin waɗanda aka kama akwai mata da miji da ke zaune a karamar hukumar Lau ta jihar Taraba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng