An Nada Dan Kabilar Ibo na Farko a Matsayin Babban Limanin Masallacin Abuja

An Nada Dan Kabilar Ibo na Farko a Matsayin Babban Limanin Masallacin Abuja

  • Mahukuntan babban masallacin Abuja sun amince da a nada sabon babban limanin masallacin da ya fara limanci a yau
  • Wannan na nufin Farfesa Iliyasu Usman zai ya shiga jerin limamai kamar su Sheikh Ibrahim Maqari da za a rika jan sallah
  • Farfesa Iliyasu Usman shi ne dan kabilar Ibo na farko da aka taba ba mukamin a babban masallacin da musulmai suke ji da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - A karon farko a tarihin babban masallacin Abuja, an nada dan kabilar Ibo a matsayin babban limami.

Mahukuntan babban masallacin sun amince da nadin Farfesa Iliyasu Usman a matsayin sabon limanin, lamarin da ya yi wa musulman Kudu maso Gabas dadi ainun.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi magana da jin labarin Ibo ya zama limami a babban masallacin Abuja

Maqari
An nada sabon babban limanin masallacin Abuja Hoto: Mu'az Magaji
Asali: UGC

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa ana sa ran sabon babban limanin, Farfesa Iliyasu Usman zai jagoranci hudubar sallar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musulmi sun ji dadin nada Ibo sabon limami

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa kungiyar Musulmi ta shiyyar Kudu maso Gabas ta yi na'am da nadin Farfesa Usman.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Juma'a, ta ce nadin Farfesa Iliyasu Usman tamkar dora kwarya a gurbinta ne.

Nadin limancin: An yabi jagorancin Sarkin Musulmi

Kungiyar Musulmin kasa a Kudu maso Gabas ta yabawa salon jagorancin Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Sa'ad Abubakar III bisa nadin sabon limanin masallacin Abuja.

Kungiyar ta ce nadin da aka yi na duba cancanta ba tare da la'akari da kabila ba zai taimaka wajen kara hade kan musulmin kasar nan.

Kungiyar na ganin haka zai kara dankon zumunci tsakanin musulmi yan kabilar Ibo da sauran musulmi a sauran shiyyoyin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.