"Mu Haɗa Karfi da Karfe," Gwamna Ya Faɗi Hanya 1 da Za a Yi Maganin Ƴan Bindiga
- Malam Uba Sani ya ce lokaci ya yi da za a haɗa karfi da ƙarfe domin kawo karshen ƴan bindiga a Arewa maso Yamma
- Gwamnan Kaduna ya buƙaci a kafa tsarin haɗin guiwa tsakanin jihohin Arewa domin zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya
- Ya kuma yabi gwamnatin tarayya bisa amincewa da kafa rundunar Operation Fansan Yamma, ya ce hakan ya nuna da gaske ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi kira da a hada karfi da karfe domin yaki da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Gwamna Uba Sani ya nuna cewa lokaci ya yi da za a ajiye komai a gefe, a haɗa hannu wuri guda wajen yaƙi da ƴan bindiga.
Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai bukatar haɗin guiwa" - Gwamna Uba Sani
Gwamna Sani ya jaddada bukatar samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin jihohin Arewa domin magance matsalar rashin tsaro da ta hana mutane sakat.
Ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kafa rundunar hadin gwiwa da Operation Fansan Yamma, ya ce hakan ya nuna gwamnati da gaske take yi.
Uba Sani ya ce wannan ziyara da ministan tsaron ya kawo tana da alaƙa da shirye-shiryen kaddamar da rundunar Operation Fansan Yamma.
Gwamna ya nemi a magance tushen rashin tsaro
Gwamnan ya kuma nanata bukatar magance tushen matsalar tsaro ta hanyar bunƙasa harkokin noma, ilimi, samae da ababen more rayuwa da haɗa kan jama'a.
Gwamnan ya roki ministan tsaro da ya duba yiwuwar kawo Operation Safe Haven karkashin runduna ta daya da ke Kaduna, domin inganta harkar tsaro.
Badaru ya yabawa sojoji a Kaduna
A nasa ɓangaren, ministan tsaro ya tabbatarwa Uba Sani cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa masa domin kakkaɓe duk wani nau'in ta'addanci a Kaduna.
Ya kuma yabawa dakarun sojoji bisa namijin ƙoƙarin da suka yi a lokacin da ya kai ziyara runduna ta daya da sasanin atisayen sojojin sama a Kaduna, Channels tv ta ruwaito.
Kaduna: Sojoji sun kashe ƴan bindiga
Kuna da labarin dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu ƴan bindiga mutum biyu har lahira a jihar Kaduna.
Sojojin sun sheƙe ƴan bindigan ne lokacin da suka je ɗaukar kuɗin fansa na wasu mutum huɗu da aka dauke.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng