Arzikin Dangote Ya Karu da Naira Tiriliyan 24.5, Ya Kara Matsayi a Jerin Attajiran Duniya

Arzikin Dangote Ya Karu da Naira Tiriliyan 24.5, Ya Kara Matsayi a Jerin Attajiran Duniya

  • Hamshakin dan kasuwar Najeriya, Aliko Dangote ya samu karuwar arziki daga dala biliyan 13 zuwa dala biliyan 27 kwanan nan
  • A bayan nan ne Johann Rupert ya zama attajirin Afrika bayan arzikin Dangote ya yi kasa, amma yanzu attajirin ya kwace kambun
  • Dangote ya samu sabon matsayi a jerin attajiran duniya da dukiyarsa ta ninku bayan fara aikin matatar mansa da ke garin Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Arzikin attajirin dan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote arzikin ya karu sosai daga dala biliyan 13 zuwa dala biliyan 27.8

An ce arzikin Dangote ya ninku ne a 'yan kwanakin nan bayan sabuwar matatar mansa da ya gina a Legas ta fara aiki.

Kara karanta wannan

"A rage ciki:" Ministan Tinubu ya ce babu kudi a kasa, ya aikawa magidanta shawara

Hamshakin dan kasuwar Najeriya, Aliko Dangote ya samu ribar $15bn a cikin 'yan kwanaki
Aliko Dangote ya samu karuwar arziki, ya sake zama na 1 a masu kudin Afrika. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Arzikin Aliko Dangote ya ninku

Wani rahoto da Bloomberg ta fitar ya nuna yanzu Aliko Dangote ya fi kowane lokaci arziki bayan ya gamu da tarin kalubale a kan hanyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban san abin da muke ginawa zai zama dodo ga wasu ba," in ji attajirin Afrika yayin wata ziyara da ya kai New York kwanan nan.

A cewar alkaluman attajiran duniya na kai tsaye da mujallar ke fitarwa, arzikin Dangote yanzu ya kai dala biliyan 27.8.

Alkaluman sun nuna matsayin Dangote ya canja ne bayan samun karuwar arziki da dala biliyan 15.1, yayin da ribar da ya samu a shekarar ya kai dala biliyan 12.7.

Dangote ya samu sabon matsayi

Yanzu dai Dangote shi ne na 65 a jerin attajiran duniya, inda ya ke da nisa daga matsayi na 175 da ya rike lokacin da ya ke da dala biliyan 13.2 a makonni kadan baya.

Kara karanta wannan

Yadda tsohon sanata ya rasu jim kadan bayan kammala addu'o'i a gadon asibiti

Kafin samun wannan nasara, Dangote ya samu kalubale, ya yi asarar sama da dala biliyan daya a watan Yulin 2024.

Tun a watan Agusta ne arzikin Dangote ya gaza haura dala biliyan 13.4, wanda hakan ya sa Johann Rupert na Afirka ta Kudu ya zama mafi arziki a Afirka.

Sai dai tun bayan da matatarsa ta fara aiki gadan gadan, Dangote ya samu ninkuwar arziki, inda a yanzu ya kwace kambun mafi arziki a Afrika kuma na 65 a duniya.

Jami'o'i 7 da suka karrama Aliko Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa manyan jami'o'in cikin gida da na waje sun karrama hamshakin mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote.

Tun daga Najeriya har zuwa Birtaniya, wadannan jami'o'i sun gamsu da tasirin Dangote kan cigaban tattalin arziki da ayyukan jin kai a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.