"A Rage Ciki:" Ministan Tinubu Ya ce Babu Kudi, Ya Aikawa Magidanta Shawara

"A Rage Ciki:" Ministan Tinubu Ya ce Babu Kudi, Ya Aikawa Magidanta Shawara

  • Gwamnatin tarayya ta shawarci yan kasar nan da su rika nutsuwa tare da buga lissafi kafin kashe kudinsu a halin yanzu
  • Ministan kasafi da tsare-tsare, Abubakar Atiku Bagudu ya bukaci a rika sayen iya abubuwan da su ka zama dole ana bukata
  • Ya nanata cewa duk da yanzu ana jin jiki a kasar nan, amma gyaran tattalin arzikin kasa ya gaji shan wahala da farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Abubakar Atiku Bagudu ya ce dole yan kasar nan su sake lissafi wajen yin cefane.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi yadda za ta raba yan Najeriya miliyan 100 da talauci

Ministan ya ce kamata ya yi jama'a su rika zama da iyalansu ana gayawa juna gaskiya kafin sawo kayayyakin amfanin yau da kullum.

Bagudu
Ministan Tinubu ya bukaci yan Najeriya su rika kashe kudi da lissafi Hoto: Sen. Abubakar Atiku Bagudu
Asali: Facebook

Tashar Channels Television ta wallafa cewa Ministan ya fadi haka ne a ranar Laraba bayan taronsu da kungiyar kwadago kan wahalar da yan kasa ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tinubu ya ce ana rashin kudi

Ministan kasafi da tsare-tsare, Abubakar Atiku Bagudu ya ce ya kamata yan kasar nan su kwana da sanin cewa Najeriya ba ta da kudin da su ke tsammani.

Ya ce saboda haka a rika zama ana tacewa kafin a sayi kayan amfani a gida, inda ya shawarci jama'a su rika gayawa junansu gaskiya.

"Tinubu na kokari:" Atiku Bagudu

Atiku Bagudu ya bayyana cewa manufofin Bola Ahmed Tinubu da ake ganin su na jawo matsin rayuwa a yanzu za su haifar da da mai ido.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

A ganinsa, tuni kasar nan ta fara ganin alfanun manufofin ta hanyar farfado da tattalin arzikin kasa da samun cigaba.

Tsohon Sanata ya yi tir da manufofin Tinubu

A wani labarin kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya caccaki manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa za su kashe yan kasar nan.

Sanata Shehu Sani ya fadi haka ne a matsayin martani ga Bankin Duniya, wanda ya bayar da shawara kan cigaba da amfani da manufofin har na tsawon shekaru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.