'Rashin Darajar Naira Ka Iya Zama Alheri ', CBN Ya Fadi Yadda Za a Inganta Najeriya
- Duk da karyewar darajar Naira a Najeriya, Babban Banki watau CBN ya bayyana yadda hakan zai iya zama alheri
- Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso ya ce duk da rashin darajar Naira akwai damarmaki da dama kan haka
- Legit Hausa ta yi magana da wani malami kuma masanin tattalin arziki kan abin da Babban Bankin CBN ya ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan rashin darajar Naira a faɗin kasar.
Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso ya fayyace amfanin Naira duk da rashin darajar da take da shi.
Naira: Bankin CBN ya ba yan Najeriya shawara
Daily Trust ta ce Cardoso ya bayyana haka ne a jiya Laraba 16 ga watan Oktoban 2024 yayin wani taro a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan CBN ya ce rashin darajar Naira zai ba Najeriya damar bunƙasa fitar da kayanta zuwa ketare.
Bankin CBN ya ce akwai damarmaki da mutane za su yi amfani da su duk da rashin darajar kuɗin a kasuwa.
CBN ya ce akwai damarmaki duk faduwar Naira
"Abin da ya kamata mu yi a yanzu shi ne tabbatar da kasancewar masu zuba hannun jari a nan saboda rashin hakan barazana ne."
"Amma kuma hakan wata dama ce da zamu bunkasa harkokin fitar da kaya ketare."
"Hakan zai kara tabbatar da Najeriya cikin gasa da sauran ƙasashe kan kasuwanci da fitar da kayayyakinta."
- Olayemi Cardoso
Cardoso ya ce yana amfani da damar domin karawa mutane karfin guiwar cewa akwai damarmaki duk da matsalar farashin Naira, cewar Tribune.
Legit Hausa ta tattauna da masanin tattalin arziki
Legit Hausa ta yi magana da wani malami kuma masanin tattalin arziki kan abin da Babban Bankin CBN ya ce.
Lamido Bello ya bambanta da maganar CBN inda ya ce hakan kara ruguza tattalin arziki zai yi.
Lamido ya ce duk lokacin da darajar Naira ya fadi jefa al'umma yake cikin mummunan yanayi.
"Babu wani saurin habaka tattalin arziki da zai kawo, sai dai ma ya kara jefa al'umma cikin asara sakamakon darajar kudin ya fadi warwas."
"Hakan zai saka a samar da kayayyaki ne da tsada sannan wanda yake da dalolinsa kalilan sai ya saye, haka kuma za'a a yi ta amfani da jama'ar kasa musamman wajen ayyuka domin samar da abubuwa ga kamfanoni."
- Lamido Bello
Naira ta sake faduwa a kasuwar duniya
Kun ji cewa Naira ba ta ji da daɗi ba a hannun Dalar Amurka a kasuwar ƴan canji a ranar Juma'a, 27 ga watan Satumban 2024.
Darajar Naira ta koma N1,700/$ wanda wannan ita ce faɗuwa mafi muni da ta yi tun daga watan Fabrairun 2024 da muka ciki.
Sai dai a farashin gwamnati, darajar Naira ta ƙaru da kaso 2.24% daga kan farashin da aka sayar da ita a ranar Alhamis 16 ga watan Oktoban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng