Magana Ta Kare, Sanatoci Sun Raba Gardama Kan Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

Magana Ta Kare, Sanatoci Sun Raba Gardama Kan Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

  • Ƴan majalisar dattawa sun jaddada goyon bayansu da suka kaɗa kuri'ar amincewa da shugabancin Sanata Godswill Akpabio
  • Sanatocin sun ɗauki wannan matakin biyo bayan yaɗuwar rahoton da ke cewa suna shirin tsige shugaban majalisar dattawa
  • Tun farko dai wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa sanatoci na ƙulla yadda za su sauke Akpabio, lamarin da fadar shugaban ƙasa ta fito ta ƙaryata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanatoci sun kawo karshen duk wata jita-jita a ake yaɗawa, sun kaɗa kuri'ar amincewa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa wasu rahotanni cewa ƴan majalisar dattawa na shirye-shiryen tsige Akpabio daga muƙaminsa.

Kara karanta wannan

Magidanci a Kano ya shiga matsala bayan ya raunata matarsa a wuri mai daraja

Godswill Akpabio.
Sanatoci sun jaddada mubaya'arsu ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Rahoton The Nation ya tattaro cewa a jiya Laraba, wasu kafafen watsa labarai sun yaɗa labarin cewa fadar shugaban ƙasa ta tura dakarun DSS zuwa majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahotannin, an tura jami'an ne domin hana sanatoci aiwatar da wasu ayyuka ciki har da yunƙurin tsige shugaban majalisar Sanata Akpabio.

Sanata Akpabio dai ya musanta jita-jitar tun farko, inda ya bayyana cewa kan sanatoci a haɗe yake, babu wani abu mai kama da shirin tsige shi.

Ita ma fadar shugaban kasa, a wata sanarwa da ta fitar ta ce babu wata barazanar tsige Akpabio a majalisar dattawa.

Karin bayani na nan take...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262