Kashim Shettima Ya Dura Sweden da Wasu Jiga Jigan Gwamnati, Bayanai Sun Fito

Kashim Shettima Ya Dura Sweden da Wasu Jiga Jigan Gwamnati, Bayanai Sun Fito

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ya isa kasar Sweden a yayin wata ziyarar aiki
  • Kashim Shettima ya samu rakiyar manyan yan siyasa ciki har da gwamna da ministan harkokin kasashen wajen Najeriya
  • Shettima zai wakilci shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kasancewar Tinubu na hutun mako biyu a kasashen Birtaniya da Faransa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa tawagar Najeriya karkashin Kashim Shettima ta isa kasar Sweden.

Sanata Kashim Shettima ya tafi Sweden ne domin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a madadin Bola Ahmed Tinubu.

Shettima
Tawagar Najeriya ta isa Sweden. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wallafa a Facebook cewa ya samu rakiyar wasu manyan jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya isa kasar Sweden

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya isa kasar Sweden domin wani aiki na kwanaki biyu.

A yau Alhamis, 17 ga watan Oktoba Kashim Shettima ya dura Sweden tare da rakiyar wasu manyan jami'an gwamanti.

Mataimakin shugaban kasar zai wakilci Bola Ahmed Tinubu da yake hutun mako biyu a kasashen Birtaniya da Faransa.

Jami'an gwamnatin Najeriya da suka tafi Sweden

A cikin tawagar mataimakin shugaban kasar akwai gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang.

Haka zalika ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar na cikin waɗanda suka raka mataimakin shugaban kasar.

Tattaunawar da Shettima zai yi a Sweden

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa cikin abubuwan da zai tattauna akwai lamarin kasuwanci da bunkasa alakar Najeriya da Sweden.

A karkashin haka, Kashim Shettima zai tattauna da Sarauniyar Sweden da kuma Firaministan kasar yayin ziyarar.

Kara karanta wannan

Ana kewar rashin Tinubu, Shettima zai shilla ketare, an samu bayanin tafiyar

Ana fatan cewa alakar Najeriya da Sweden za ta kara karfi bayan kasashen sun tattauna a kwanki biyu.

Abubuwan da suka faru yayin hutun Tinubu

A wani rahoton, mun tatttaro muku cewa bayan tafiyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yan Najeriya sun tattauna abubuwa da dama.

Cikin abubuwan akwai jita jitar cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya tafi Birtaniya ne domin jinya da kuma karin kudin litar man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng